24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

2023:Jam’iyyar PDP ta fitar da jaddawalin Kudaden Tikitin takarar kowace kujera

Labarai2023:Jam'iyyar PDP ta fitar da jaddawalin Kudaden Tikitin takarar kowace kujera
PDP1
Jam’iyyar PDP ta fitar da kudaden kowace kujerar takara

Jam’iyyar ta bayyana haka ne a wani taro da ya gudana

Jam’iyyar ta amince da hakan ne a babban taron jam’iyyar na kasa karo na 95 da aka gudanar a ranar Laraba a Abuja.

Jam’iyyar ta kuma amince da fara sayar da fom din daga ranar Alhamis, 17 ga watan Maris domin babban zaben shekarar 2023.kujerar takarar shugaban kasa an kayyade Naira Miliyan 35 a matsayin kudin tikiti,sai kuma kudin sha’awar tsayawa takarar Naira Miliyan 5.

Masu neman takarar gwamna za su biya Naira Miliyan 41

A bisa ka’idojin da aka fitar a ranar Laraba, An tsaida cewa ‘yan jam’iyyar masu neman kujerar gwamna za su biya Naira Miliyan 20 kudin tikiti sai kudin nuna sha’awar takara Zasu biya Miliyan 1 Sai kuma kudin Fidda gwani Naira Milliyan 20.

Masu neman takarar Sanata za su biya Miliyan 3.5

Masu neman takarar Sanata za su biya Naira 500,000 kudin nuna sha’awar takara Sai kuma Naira Miliyan 3 na Tikiti

Yan takarar Majalisar wakilai za su biya Miliyan 2.5

Haka kuma, ‘yan takarar majalisar wakilai za su biya Naira 2.5, tare da kudin nuna sha’awar takara Naira 500,000 sai kudin tikitin tsayawa takara a kan N2m.

Masu neman takarar majalsar dokokin jiha

Masu neman takarar majalisar dokokin jiha za su biya Naira 100,000 kudin sha’awar tsayawa takara da kuma Naira 500,000 na tikitin tsayawa takara.
Hakazalika jam’iyyar ta amince da rage kashi 50 cikin 100 na kudaden takara ga matasa da basu wuce shekaru 25 zuwa 30 na mukamai daban-daban.

Hukumar zabe ta kasa(NEC) ta kuma amince da kafa kwamitin shiyya mai wakilai mutum 37 domin bayar da shawarwarin yadda za a ware mukamai daban-daban na zaben shekarar 2023.

2023: Kungiyar mambobin jam’iyyar PDP ta yi barazanar sauya sheka idan aka bai wa dan arewa takarar shugaban kasa
Idan har jam’iyyar PDP ta kasa tsayar da shugabancin ƙasa daga Kudu, to akwai yiwuwar mambobin jam’iyyar za su fice daga jam’iyyar, in ji wata ƙungiyar PDP, Vanguard for Justice.

A baya-bayan nan dai jam’iyyar PDP ta musanta cewa ta mayar da tikitin kujerar shugaban ƙasa zuwa Arewa sakamakon ikirarin da tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu ya yi na cewa ta yi hakan.
Sai dai ƙungiyar a cikin wata sanarwa da shugaban ta Emmanuel Nduka ya fitar, ta gargadi jam’iyyar kan mayar da wannan matsayi zuwa yankin Arewa. Ya bayyana cewa, maida shugaban ƙasa zuwa Kudu zai samar da hadin kan ƙasa, daidaito da kuma adalci.

Bugu da kari, kungiyar ta ce yadda akasarin mutanen da ke neman mulki suka koma Kudu, ya nuna cewa abin da Najeriya ke bukata a 2023 shi ne shugaban ƙasa daga Kudu.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa@gmail.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe