29 C
Abuja
Saturday, December 3, 2022

Yaron da ya kwaikwayi gadar Kano da wasa ya samu gurbin karatu a kasar Amurka, an kuma yiwa mahaifiyarshi kyautar miliyan daya

LabaraiYaron da ya kwaikwayi gadar Kano da wasa ya samu gurbin karatu a kasar Amurka, an kuma yiwa mahaifiyarshi kyautar miliyan daya

Wani ƙaramin yaro ya zama sanadiyyar samun tagomashin iyayen sa bayan da wani kamfanin gine-gine ya lura da aikin sa.

Ƙaramin yaron ɗan Najeriya mai suna Musa Sani ya zama abin magana akan yanar gizo bayan yayi irin ɗaya daga cikin gadojin sama na Kano wanda ya gina da abubuwan da ya samo daga nan cikin gida Najeriya. Jaridar Legit.ng ta rahoto

Yaron na da ƙashin arziƙi

Da yake wallafa hotunan Musa tare da ƙirƙirarsa a shafin Twitter, wani ɗan Najeriya mai suna @OvieNews ya bayyana cewa wani kamfanin gine-gine mai suna Ronchess Global Resources, ya ba Musa gurbin karatu a jami’a a ƙasar Amurka kyauta.

@OvieNews wanda ya bayyana cewa shugaban kamfanin ya tuntuɓe sa, inda ya ƙara da cewa kamfanin ya ba mahaifiyar Musa naira miliyan ɗaya (N1m) ta fara sana’a, yayin da kuma aka ba mahaifin shi aiki a kamfanin.

Kamfanin kuma yayi alƙawarin saka ƙannen Musa a makaranta mai kyau sannan kuma za su mayar da mahaifansa zuwa wani ƙerarren gida a cikin birnin Maiduguri.

Mutane sun yaba sosai

Nuruddeen Ibrahim Kafinta yace:

MashaAllah. Wannan babbar kyauta ce daga Allah.

Centina J Aridi ya ce:

Ina taya su murna wannan labari ne mai daɗin ji, nayi farin cikin jin wannan labarin.

Eunice Alonge Obaro ya ce: 

Wannan ba wani abu ba ne; mahaifin zai je ya auri mata da yawa sannan ya ƙara haifo yara.

Sabiu Ibrahim ya ce:

Wannan abu ne mai kyau. Mu yaɗa shi domin ƙara ƙarfafa guiwar wannan yaron da kuma Ronchess Global Resources

Yaro dan shekara 15 da ya fara sana’ar sayar da riguna tun yana dan shekara 12 ya samu ribar naira miliyan 913 a shekara daya

A lokacin bikin zagayowar ranar haihuwar sa karo na 12, Trey Brown yana da ƙwaƙwalwa wacce ba kasafai ake samun ta a wajen yara masu shekarun sa ba.

Hikimar siye, gyarawa da kuma sayar da riguna ta zo masa. Ya yanke shawarar yin amfani da N73,830 ɗin da ya samu wajen bikin zagayowar ranar haihuwar sa wajen siye sannan ya gyara riguna kafin sayar da su ga mutanen yankin sa. Legit.ng ta rahoto

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe