24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

A karshe dai Abba Kyari ya fito yayi magana, ya bayyana wani boyayyen abu da NDLEA take yi a boye

LabaraiA karshe dai Abba Kyari ya fito yayi magana, ya bayyana wani boyayyen abu da NDLEA take yi a boye

Abba Kyari, dakataccen mstaimakin kwamishinan ‘yan sanda ya bayyana cewa gurɓatattun jami’an hukumsr NDLEA ne su kayi masa sharri bayan ya nemi da a bayar da kyauta ga mai tona asiri wanda ya taimakawa ‘yan sandan IRT cafke wanda ake zargi.

Abba Kyari na fuskantar shari’a

Abba Kyari wanda ya ke fuskantar shari’a a wata babbar kotu da ke Abuja bisa zargin sa hannun sa a cikin safarar hodar iblis, ya zargi jami’an NDLEA da bada kariya ga masu safarar kwayoyi zuwa cikin Najeriya. Legit.ng ta rahoto.

Abba Kyari
Abba Kyari a kotu yayin da yake fuskantar shari’a. Hoto daga legit.ng

Abba Kyari wanda a baya ya ke jagorantar  Intelligence Response Team (IRT) ya fara shiga cikin matsaloli ne tun lokacin da gwamnatin Amurka ta bada sunan shi a cikin wani laifin damfarar yanar gizo.

A yayin da gwamnatin Amurka ta buƙaci da a miƙa mata Kyari, NDLEA ta zarge shi da hannu a cikin safarar ƙwayoyi tare da sauran wasu jami’an ‘yan sanda.

Hukumar ta saki wani faifan bidiyon Abba Kyari yana ƙoƙarin ba ɗaya daga cikin jami’anta cin hanci.

Abba Kyari ya maka NDLEA kotu

Sai dai, a yayin da ake cikin ɗamke shi da kuma gurfanar sa a gaban kotu, dakataccen ɗan sandan ya maka NDLEA ƙara bisa take masa haƙƙin sa na ɗan Adam inda ya buƙaci da a biya shi naira miliyan 500 (N500m) na tauye masa damar sa ta yin tafiya da sauran su.

A wasu takardun kotu wanda wani Muhammad Nur Usman wanda ya bayyana kansa a matsayin ƙanin Abba Kyari, ya bayyana wa kotu cewa jami’an NDLEA suna kyale wani babban mai safarar kwaya “sannan su yi ma sa rakiya daga filin jirgi zuwa masaukin sa”

Abba Kyari ya ce a wannan ranar, kamar kowane lokaci wanda ake zargin ya shigo da hodar iblis daga Ethiopia zuwa filin jirgin sama na Enugu.

Cewa jami’an NDLEA sun bar shi ya wuce a cikin filin jirgin, sannan jami’in FIB-IRT ya cafke shi tare da samun taimakon bayanai

Cewa kafin mai bada bayanan ya yarda yayi aiki da jami’an FIB-IRT, sun cimma yarjejeniyar za a bashi wani kaso na ladan aikin sa.

Cewa jami’an FIB-IRT, bayan sun lura cewa jami’an NDLEA su ne su ke kyale wanda ake zargin tare da hodar iblis ɗin sa, sun garzaya miƙa wanda ake zargin ga NDLEA  tare da sunayen jami’an da su ke da hannu a lamarin.

Cewa maimakon NDLEA ta yi abinda ya dace kan lamarin ta hanyar ɗamke jami’anta masu hannu a lamarin, sai su ka yanke shawarar hasala mai bayar da bayanan ta hanyar ƙin sallamar sa.

Cewa a daidai wannan gaɓar ne aka tuntubi DCP Abba Kyari wanda jami’an NDLEA ɗin da ke da hannu abokin sa ne, shine ya sanya baki domin a sallami wanda ya bayar da bayanan.

Cewa jami’in NDLEA wanda ya ƙi sallamar mai bayar da bayanan shine yayi wa Abba Kyari sharri ta hanyar yi masa ƙagen cewa yana ƙoƙarin bashi cin hanci.

Cewa hukumar wanda ake ƙara ta ayyana tana neman wanda ke ƙara saboda zargin yana ƙoƙarin bayar da cin hanci ga jami’in NDLEA ba tare da wata ƙwaƙƙwarar shaida ba.

Cewa hukumar ‘yan sandan Najeriya, ta hanyar amfani da zargin wanda ake ƙara ta cafke wanda ke ƙara a ranar 12 ga watan Fabrairun 2022, sannan ta miƙa shi ga hukumar NDLEA.

Ana cigaba da sauraren ƙarar Abba Kyari ta neman samun ƴancin sa daga NDLEA tare da ƙarar sa kan safarar hodar iblis.

Zargin safarar hodar Iblis: Yadda Abba Kyari ya yi aiki da ƙungiyar ƙwaya a Brazil – NDLEA

Hukumar ‘yan sanda ta ba da sanarwar damƙe Abba Kyari a ranar litinin da ta gabata ne dai bayan kiran da aka yi na nemansa ido rufe game da safarar miyagun kwayoyi kamara yadda NDLEA ke zarginsa

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa, NDLEA, ta nesanta jami’anta daga cinikin hodar ibilis mai nauyin kilogiram 25 da suka haɗa kai da gungun ‘yan sanda ƙarƙashin jagorancin mataimakin kwamishinan ‘yan sanda da aka dakatar, Abba Kyari.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe