22.5 C
Abuja
Friday, December 2, 2022

Kotu a Birnin Karnataka na kasar India ta hana dalibai mata sanya Hijabi a Makaranta

LabaraiKotu a Birnin Karnataka na kasar India ta hana dalibai mata sanya Hijabi a Makaranta
Karnataka State High Court Agree To Enforce Ban On Wearing Hijab In Schools
kotu ta hana dalibai mata sanya hijabi a birnin karnataka da ke kasar Indiya

Babbar kotu a Indiya ta yanke hukunci

Yayin da Musulman Indiya ke tsaka da damuwa game da matakin ‘Hindu na farko’ da gwamnati ta yi, babbar kotun jihar Karnataka ta kasar Indiya ta kara dagula al’amura inda ta bayyana cewa ta amince a hukumance ta tabbatar da dokar hana sanya hijabi ga dalibai musulmi a makarantu.

Kotun ta ce hijabi ba wani muhimmin aikin addini ba ne a Musulunci. Don haka ba za a ba shi kariya daga sashe na 25 na kundin tsarin mulkin kasar ba, kundin da yake magana akan ‘yancin yin addini. Kotun ta kuma ce ‘yancin da jihar ke da shi na yanke hukuncin abin da dalibai za suyi ya kasance mai mutunci ne kawai.

A baya an samu barkewar rikicin sanya hijabi a wata makarantar Kwaleji

A watan Satumbar Shekarar 2021 ne rikici ya barke a wata makarantar mata ta gwamnati da ke Udupi, Karnataka, inda aka hana dalibai musulmi shiga ajujuwa saboda suna sanye da hijabi. A cewar kwalejin, saka hijabi abu ne da ake daukarsa a matsayin keta dokokin makarantar.

Dalibai sun yi zanga akan an tauye musu hakki

Abu kamar wasa yazo ya zama abin cece-kuce, har ta kai dalibai musulmai sun yi zanga-zangar cewa an tauye musu hakkinsu na yin addininsu saboda wannan doka, inda dali suka ce a baya sun kasance suna sanya hijabi a makaranta ba tare da wata matsala ba.
Lamarin ya harzuka mutane a duk fadin Indiya da kewaye inda abun ya zama babbar tambaya a tsakanin jama’a. Ba wai batun hijabi kadai ba, yawancin mutane a Indiya suna sanya tufafi na musamman saboda addininin su. Amma kamar rikicin ya fi karfi tsakanin Musulmai da Hindu a Indiya.

Kundin tsari ya ba da ‘yancin addini
Ba a kafa kasar Indiya bisa addini ba. A matsayin shaida, kundin tsarin mulkin Indiya ya kare ‘yancin yin addini. Sai dai hakan ya bambanta da abin da ake yi da Firayim Ministan Indiya, Narendra Modi da jam’iyyarsa ta siyasa, BJP (Bharatiya Janata Party).
Ya yi kokari matuka wajen ganin ya sanya bukatun mabiya addinin Hindu kusan kashi 80 sama da bukatun sauran tsirarun addinai, musamman kashi 14% na al’ummar musulmi da ke kasar.

Mista Modi har ya yi yunkurin takaita adadin musulmi a kasar yayin da ya karbe jiharJammu & Kashmir (J&K), jiha daya tilo da musulmi ke da rinjaye a Indiya. Amma sai doka kare J&K inda ta basu izinin shimfida na su dokokin.
A baya dai gwamnatin jihar Karnataka da jam’iyyar BJP ke Mulki ta goyi bayan makarantu da suka hana dalibai musulmai sanya hijabi, inda lamarin ya yi sanadiyan da aka rufe makarantu na tsawon kwanaki uku sakamakon zanga-zangar da ta barke.


Yadda wani bidiyo ya nuna ‘yan sanda a Indiya na dukan mata Musulmai da suka fito yin zanga-zangar hana su sanya Hijabi

Yayin wata zanga-zangar adawa ta dokar hana sa hijabi a Uttar Pradesh ta Ghaziabad da ke kasar Indiya an ga ‘yan sandan jihar sun farwa mata Musulmai da ke sanye da hijab da duka.

Yayin da zanga-zangar ke cigaba da gudana a wasu da ga cikin jihohin kasar a bisa kan dokar hana sa hijabi a kwalejoji, hatsaniyar ta fara ne a Karnataka wanda har ta kai ga an shiga kotu
Rundunar ‘yan sandan ta sanar da cewa ta fara gudanar da bincike kan faifan bidiyon da ya yadu a shafukan sada zumunta inda wasu suke suka tare da caccakan ‘yan sandan.
Dangane da lamarin da ya faru a ranar Lahadin da ta gabata, ‘yan sanda sun gabatar da rahoton farko game da bayanan abun da ya faru.

A rahoton da ‘yan sandan suka fitar, rundunar ‘yan sandan ta ce ta samu labarin cewa wasu matan Musulmi kimanin su 15 dauke da takardu na nuna adawa da gwamnati sun taru a hanyar Sani Bazaar a Ghaziabad ba tare da an basu izini ba. FIR ta ruwaito cewa matan sun fara rera waka ne a lokacin da tawagar ‘yan sanda ta iso wurin.
Wasu maza da suka fito daga cikin tawagar masu zanga-zangar sun fito inda suka fara cin zarafi suna zagin jami’an ‘yan sandan da ke kokarin kora masu zanga-zangar su koma gida, a cewar FIR. A cewar korafin da ‘yan sandan su ka fitar an bayyana wani mai suna Raees a matsayin daya daga cikin wadanda ake tuhuma , kuma masu zanga-zangar sun yi barazana ga ‘yan sandan.
Bidiyon ya nuna yadda ‘yan sanda suka tarwatsa masu zanga-zangar da karfi, kuma an hangi, wata mata sanye da niqab tana kokarin kare dukan da ‘yan sanda su ke kokarin yi mata da sanda a cikin bidiyon.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe