24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Wani direba da ya tsinci miliyan daya da dubu dari biyu 1.2m kuma ya mayarwa da mai shi, amma ba’a bashi ko sisi ladan tsuntuwa ba

LabaraiWani direba da ya tsinci miliyan daya da dubu dari biyu 1.2m kuma ya mayarwa da mai shi, amma ba'a bashi ko sisi ladan tsuntuwa ba

 Wani matashi dan Nageriya Emmanuel Christopher, ya dawo da kudi kimanin dala dubu uku $3,000 daidai da N1,247,520 na kudin Najeriya, wanda wata mata ta manta a matarsa bayan ya dauke ta a matsayin hayar tasi.


Duk da zugar da Shaidan ke yi masa akan ya rike dalolin, amma Emmanuel din yayi abin da ya dace, ya dawo mata da kudinta .


Yan Nageriya da dama sun ji haushin matar mai kudin, saboda bata bashi ko sisi ba na landan tsuntuwa. 


Wani matashi dan Nageriya Emmanuel Christopher, ya sha yabo a kafar sada zumunta, sakamakon makurar gaskiyar sa da ya nuna wajen dawowa da wata fasinjar sa kudadenta da ta manta a motarsa, a Abuja. 

dala dubu uku

Matar mai suna Wise Lara, wadda ta bayyana irin halin kirkin sa, a shafinta na Facebook, tace shi mutumin dan Cocinsu ne, kuma mutum ne mai matukar jajircewa. 

Daloli, fasko, da kuma sauran abubuwa masu daraja

A fadar ta, tace a lokacin da Emmanuel ya sauke fasinja mace a birnin tayya, can sai ya fahimci kamar ta manta wata jaka mai dan kumari, a kujerar baya. 

Bashi da tabbacin ta waye, kawai sai ya bude jakar, inda yaci karo da daloli, da sauran kudaden kasar waje. 


Ya iya lissafa sama da dala dubu uku $3,000 daidai da kudin Najeriya N1,247,520, da kuma wasu sauran kudaden kasashen waje. Banda ma kudin, dan tasi din ya ga katin ATM guda uku, da kuma fasko na kasashen waje guda uku. 

Ya sha zugar Shaidan akan ya gudu da kudin


Da yake yi mata jawabi akan yadda abin ya faru, da kuma yadda Shaidan ya dinga zuga shi akan ya rike kudin; sai yace: 

“Zuciya ta tayi mini magana, ni ma kuma na bata amsa


Lokacin da Emmanuel ya dawo wa da matar kudin, ta girgiza sosai, inda ta kama zubar da zafafan hawaye, amma bata bashi ko sisi a matsayin ladan tsuntuwa ba. 


Amma shi duk da haka, Emmanuel yace hankalin sa yafi kwanciya da abin da yayi na dawo mata da dukiyar ta. 
Ga kadan daga cikin sharhin da akayi akan lamarin : 


Larry Dee cewa yayi 

” Wannan gayen ya cancanci a rama masa ke Lara zaki iya adana bayanan sa na banki “

Matar Emmanuel mai suna  Favour Oluebube, ta yi sharhi, inda take cewa  :

” Masoyi, ai mun gwammace mu mutu da yunwa, akan muci abin da ba hakkin mu ba. Ina tayaka murna masoyi, Yesu da sauran masaukan aljanna suna alfahari da kai. Ina sonka masoyi na kai ne mafi dacewa ” 


Bishop Irabor Wisdom yace :

” Kai ! Wannan wacce irin mata ce mara godiya, ko irin kyautar nan ta na gode, gaskiya dai wannan bata ji dadinta ba. Amma babu komai, shi kuma Emma karka damu  ! Ba lallai ne mu girbi a inda muka yi shuka ba amma tilas mu girbi abin da muka shuka” 

 Àlàbá Olúwasanmílęsanre Olásúnkànmí yace : 

“Allah ya yi masa albarka, 

Ina tsoron ranar haduwa ta da Allah, cewar Taver Tersugh matashi da ya mayar da makudan kudin da aka yi kuskuren tura masa

Irin yadda gaskiya da Amana ta yi karanci ba kasafai ba ne matashi zai maida abunda ba na shi ba. Wani dan Najeriya mai suna Taver Tersugh James ya mayar da kudi naira 10,000 da wani ma’aikacin POS ya tura mishi a bisa kuskure. Lamarin ya faru ne a Makurdi, babban birnin jihar Benuwai.

Wani bayani da Legit.ng ta samu ya nuna cewa ana shirin tuhumar mai aiki a POS din kenan a daidai lokacin da Taver Tersugh ya yanke shawarar mayar da kudin.

Abokai sun bani shawarar kar in mayar da kudin

Matashi Taver ya ce wasu abokansa sun gaya masa cewa kudin da aka turo masa Allah ne ya ciyar da shi. Ya ce sun ba shi shawarar kada ya mayar.
Duk da haka, bai yadda yadauki shawarar su ba maimakon haka sai ya yanke shawarar kai kuɗin ga wakilin POS din.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe