24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Bidiyon Yadda Wani Mutum Ya Shiga Banki Ya kwashe musu Na’urar firinta, saboda bashin da ya ke bin banki

LabaraiBidiyon Yadda Wani Mutum Ya Shiga Banki Ya kwashe musu Na'urar firinta, saboda bashin da ya ke bin banki
ca8ac8f5f41715a2
mutumin da ya wawuri na’uara banki saboda yana binsu bashi

Ya shiga Banki a fusace

Wani dan mutum ya tari aradu da ka inda ya shiga banki ya wawuri daya daga cikin na’urar firintar su, inda yace ba zai ajiye ba sai sun saurareshi. An ga mutumin a cikin wani faifan bidiyo yana kokarin yin awon gaba da na’urar amma sai dai mutane sun sa shi gaba suna rokon shi da ya dakata. Shi kuma ya bada sharadin ba zai ajiye ba har sai bankin sun shirya saurarar shi.

Ya na bin Banki bashin kudi

Kamar yadda bayanai suke fitowa da ga bakinshi a cikin faifan bidiyon, mutumin ya yi ikirarin cewa ya na bin bankin kudi sun ki biyan shi ko kuma sun ki su kula da shi tsawon watanni biyu kenan.
Lokacin da ya bude kofar bankin zai fita da na’urar rike a hannun sa,wasu mutane sun yi kokarin lallashinsa. Sai ya tsaya ta re da aikawa da ma’aikatan bankin tambaye “Shin kun shirya saurara ta ?” Sai dai mutumin ya ba da,umurnin kada kada wanda ya roke shi. Saboda yana so yasan aron kudi ya ke ba wa bankin ko kuwa yana da matsala ne da ma’ajiyarsa da kuma wurin cire kudi.

Kadan daga cikin martanin mutane

thugger_147 ya ce “Wannan ƙasar ya kamata a yi zango na 7 kashi na 14 na Netflix.”

@official_zinny23 ya sake cewa: “hakan da ya yi shine dai dai.”

@fashion_magicblog ya ce: “Ba koyaushe nake goyon bayan tashin hankali ba amma za ku ga yadda zai sami kudinsa da sauri, in da ya yi shiru ba mai sauraron sa…Lol.”

@joelilyofficial ya ce: “Ahhhhh. Abun bai kai ga haka ba dan uwa.”

@dullahyaro yayi sharhi: ” wai Dole sai mutum ya nuna bakin hali kafin banki su saurari mutun game akan kudinsa, wannan wane irin wahala ne”

Ina tsoron ranar haduwa ta da Allah, cewar Taver Tersugh matashi da ya mayar da makudan kudin da aka yi kuskuren tura masa


Irin yadda gaskiya da Amana ta yi karanci ba kasafai ba ne matashi zai maida abunda ba na shi ba. Wani dan Najeriya mai suna Taver Tersugh James ya mayar da kudi naira 10,000 da wani ma’aikacin POS ya tura mishi a bisa kuskure. Lamarin ya faru ne a Makurdi, babban birnin jihar Benuwai.

Wani bayani da Legit.ng ta samu ya nuna cewa ana shirin tuhumar mai aiki a POS din kenan a daidai lokacin da Taver Tersugh ya yanke shawarar mayar da kudin.
Matashi Taver ya ce wasu abokansa sun gaya masa cewa kudin da aka turo masa Allah ne ya ciyar da shi. Ya ce sun ba shi shawarar kada ya mayar.
Duk da haka, bai yadda yadauki shawarar su ba maimakon haka sai ya yanke shawarar kai kuɗin ga wakilin POS din. Ga sakon da aka aika wa Legit.ng in da yake cewa:

“Wani matashi mara aikin yi a jihar Benuwe mai suna Taver Tersugh James ya mayarwa ma’aikacin POS da ke Makurdi babban birnin jihar Benuwe kudi 10,000 da aka turo masa ba bisa ka’ida ba.
“Ya bayyana cewa a koda yaushe yana sha’awar zama sanadiyar alheri ga wani amma ba tsiya ba wanda zai iya janyo fushin Ubangiji. Ya kara da cewa wasu daga cikin abokan sa sun ba shi shawarar da kada ya mayar da kudin inda suka jaddada masa cewar wannan wata hanya ce da Ubangiji ya ciyar da shi amma sai yaki bin maganar su, suma kuma ya ya musu nasiha a kan wannan mummunar dabi’a domin samun cigaba a cikin al’umma.
Duba da irin yadda Rayuwa ta yi tsada, ya kara da cewa amma na san Allah zai kawo sauki. Wakiliyyar POS wanda maigidan ta ya yi barazanar zabtare kudin daga cikin albashin ta, ta bayyana matashin a matsayin mutum mai kyakywan niyya ga al’umma.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe