27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Wahalar man fetur: Mamaki ya kama mutane bayan ganin bidiyon wani mutum yana zuba wa mota fetur yayin da take tafiya

LabaraiWahalar man fetur: Mamaki ya kama mutane bayan ganin bidiyon wani mutum yana zuba wa mota fetur yayin da take tafiya

A yayin da ƙarancin man fetur ke ƙara ƙamari a Najeriya, mutane sun koma amfani da hanyoyi masu haɗari domin samun man fetur ɗin.

Hanya ta baya-bayan nan cikin hanyoyi masu haɗarin gasken itace ta zuba man fetur ɗin cikin mota yayin da ta ke tsaka da tafiya kamar yadda aka gani a wani bidiyo da ya karaɗe yanar gizo.

Lamarin ya faru ne a Abuja

Bidiyon an ɗauke shi a birnin tarayya Abuja. Mai sayar da man fetur ɗin wanda ɗan bumburutu ne an ganshi yana gudu yana bin motar yayin da ya ke zuba man fetur ɗin cikin tankin motar.

Mutane da dama sun bayyana wannan hanyar da mutumin yabi a matsayin mai haɗarin gaske a gare shi da kuma direban motar. Kafar @instablog9ja ta wallafa bidiyon.

Bidiyon zuba man fetur ɗin ya ɗauki hankulan mutane

A lokacin da bidiyon ya karaɗe shafin Instagram, nan da nan ya jawo hankulan mutane da dama. Ga kaɗan daga ciki da mu ka tattaro mu ku anan ƙasa:

@olamiteebo ya rubuta:

Ku na wasa da rayuwar ku

@kasali_wells ya rubuta:

Har yanzu abubuwa na baku mamaki a Najeriya.

@isoa_iyomon ya rubuta:

Mutanen Legas sun shigo Abuja.

@officialdanielrolland ya rubuta:

Idan wuta kama yanzu sai kuma ku ɗorawa shaiɗan laifi.

@sandiepearls_ ya rubuta:

Mutane na na Abuja ku hanzarta zuwa ina neman ku.

@oluwakemi._o ya rubuta:

Wasa mai haɗarin gaske, idan wajen ya ƙone waɗanda ba suji ba basu gani ba abin zai ritsa da su.

Mamaki ya mamaye zukatan mutane bayan yaduwar hotunan mata mai shekaru 40 da ta haifi yara 44

Bayan yaduwar hotunan wata mata da ta haifi yara 44, mutane da dama sun dinga cece-kuce su na mamakin irin arzikin yaran da Allah ya bata.

Cikin yaran matar wacce ake yi wa lakabi da Mama Uganda, akwai maza 22 da mata 16 kasancewar 6 sun rasu.
Kuma babban abin ban sha’awar shine yadda take kulawa da duk yaran bayan mijinta ya yashe kudadensu ya tsere ya barta.

Matar wacce ‘yar asalin kasar Uganda ce ta fara haihuwa tana da shekaru 13 bayan iyayenta sun yi mata aure lokacin ta na da shekaru 12 a duniya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe