24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

‘Yan bindiga sun halaka DPO, ‘yan sanda biyu da ‘yan sakai huɗu a jihar Neja

Labarai'Yan bindiga sun halaka DPO, 'yan sanda biyu da 'yan sakai huɗu a jihar Neja

‘Yan bindiga a ranar Talata sun kai hari ƙauyen Nasko cikin ƙaramar hukumar Magama ta jihar Neja, inda su ka halaka Divisional Police Officer (DPO), Chief Superintendent of Police (CSP) Umar Mohammed Dakingari, ‘yan sanda biyu da wasu ‘yan sakai mutum huɗu. Jaridar Independent.ng ta rahoto

‘Yan bindigan sun dawo ɗaukar fansa

Wata majiya ta bayyana cewa ‘yan bindigan sun dawo ɗaukar fansa ne bayan an kai musu farmaki a wajen ɓuyar su sannan aka ƙwato shanaye a hannun su.

Ba a daɗe ba, DPO ya jagoranci tawagar ‘yan sanda da kuma ‘yan sakai a wani aiki wanda yayi sanadiyyar halaka ‘yan bindiga da dama da kuma ƙwato shanaye sama da 800.

Yana cikin ganawa da jami’an sa domin kitsa wani sabon aikin lokacin da ‘yan bindiga su ka mamaye ofishin ‘yan sandan sannan su ka fara harbi kan mai uwa da wabi.

An bindige DPO, tare da jami’an sa da misalin ƙarfe uku na rana a ofishin ‘yan sanda na Nasko cikin ƙaramar hukumar Magama.

Duk da dai sun halaka DPO, da wasu ‘yan sanda biyu, sauran ‘yan sandan da su ka kawo ɗauki sun daƙile harin inda fatattaki ‘yan bindigan tare da munanan raunika.

Hukumar ‘yan sanda ta yi magana

Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya bayyana cewa DPO da ‘yan sanda biyu tare da ‘yan sakai mutum huɗu sun rasu a yayin musayar wuta.

Abiodun ya bayyana cewa:

A ranar 15/03/2022  da misalin ƙarfe uku na rana, ‘yan bindiga ɗauke da makamai sun kai farmaki ƙauyen Nasko a cikin ƙaramar hukumar Magama ta jihar Neja

Nan da nan DPO ɗin Nasko ya haɗa jami’an ‘yan sanda da ‘yan sakai sannan su ka tunkari ɓata garin a wata musayar wuta inda aka halaka wasu daga cikin ɓata garin yayin da wasu su ka gudu da raunika. Abin takaici, a yayin musayar wutar, DPO da ‘yan sanda biyu tare da ‘yan sakai mutum huɗu sun rasa rayukan su.

Ya bayyana cewa ‘Area Commander’ na Kontagora, ya tura jami’ai tare da sojoji zuwa ƙauyen domin tabbatar da doka da oda.

Ya bayyana cewa hukumar ‘yan sanda tana miƙa sakon ta’aziyar ta ga iyalan ‘yan sandan da na ‘yan sakai waɗanda su ka rasa rayukan su, sannan kuma ya tabbatarwa da al’umma cewa hukumar ba za ta yi ƙasa a guiwa ba wajen ƙoƙarin ta na daƙile ta’addanci a jihar.

Yan bindiga sun yi awon gaba da amarya akan hanyar kai ta gidan miji a jihar Neja

Wata sabuwar amarya ta faɗa a hannun ‘yan bindiga akan hanyar kai ta zuwa gidan mijin ta a jihar Neja.

Jaridar Daily Trust ta samo cewa ‘yan bindigan sun kawo harin ne lokacin da ‘yan’uwan amaryar su ka ɗauko ta daga ƙauyen Allawa a ƙaramar hukumar Shiroro zuwa garin Pandogari, a ƙaramar hukumar Rafi ta jihar.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe