29 C
Abuja
Saturday, December 3, 2022

Yadda Jaruma Maryam Yahaya ta dauki wanka mai zafi a wurin dinar tsohon saurayinta, Abubakar Mai Shadda

LabaraiKannywoodYadda Jaruma Maryam Yahaya ta dauki wanka mai zafi a wurin dinar tsohon saurayinta, Abubakar Mai Shadda

Yayin da ake shagalin bikin fitaccen furodusan Kannywood, Abubakar Bashir Mai Shadda, jaruma Maryam Yahaya, wacce tsohuwar budurwarsa ce ta ba kowa mamaki, Tashar Tsakar Gida ta ruwaito.

Hausawa su kan ce “kishi kumallon mata”, sai dai a bangaren Maryama Yahaya, ta nuna cewa sam ba hakan bane.

maryam yahaaa
Yadda Jaruma Maryam Yahaya ta dauki wanka mai zafi a wurin dinar tsohon saurayinta, Abubakar Mai Shadda

Domin ta bayyana a wurin bikin wanda aka kwashe ranaku da dama ana shagulgula iri-iri, inda ta dauki wanka mai burgewa.

Duk shagalin da aka yi sai da ta yi anko kuma ta nuna murnar ta ta hanyar girgijewa inda ta dinga tikar rawa wanda ya ba kowa mamaki.

Jarumai, mawaka da sauran mutane ‘yan uwa da abokan arziki sun yi cincirindo wurin zuwa bikin wanda aka dinga barin nairori.

Manya a industiri irin su Ali Nuhu, Rarara, Adam A. Zango da sauran su duk sun yi masa kara wanda hakan yasa bikin ya dauki hankali kwarai.

A bangaren manyan mata kamar Saratu Gidado wato Daso, Teema Makamashi, Hadizan Saima da sauran su duk sun halarci bikin. Hatta tsofaffin jarumai kamar su Fati Bararoji, Masura Isah duk sun je.

Sai dai lamarin bai bayar da mamaki ba saboda wannan ne karo na farko tsawon lokaci da dan fim ya auri ‘yar fim, hakan yasa kowa yake mararin zuwa don shagali ne na tuwo na mai na ne.

Bayyanar Maryam Yahaya, tsohuwar budurwar ango ya yi matukar ba mutane mamaki, saboda ba a yi tunanin zata je ba saboda wasu dalilai.

Tun da aka fara shirye-shiryen bikin mutane suka dinga tsegunguma har ta WhatsApp akan cewa ba a ga Maryam Yahaya ta wallafa katin gayyata ko kuma ta taya ma’auratan murna ba.

Wasu suka dinga tambayar cewa ko dai kishi ne ya hana ta wallafawa saboda kusan duk wasu ‘yan masana’antar suna ta wallafawa tare da yi musu fatan alheri.

Kwatsam sai ga Maryam Yahaya sanye da ankon bikin cike da murna inda ta bayyana a wurin shagalin wanda hakan ya yi matukar bayar da mamaki.

Ta wallafa hotunan a shafinta na Instagram:

Sai dai a bangaren rawa ba ta zake ba balle ace ta yi wani abu saboda kishi ko kuma bakin ciki.

Da fatan Allah ya ba wa ango da amarya zaman lafiya, ameen.

Sabbin hotunan Maryam Yahaya a Dubai babu rigar mama sun janyo mata zagi

A ranar Juma’a, 18 ga watan Fabrairun 2022 jarumar Kannywood, Maryam Yahaya ta saki sabbin hotunan ta a shafin ta na Instagram ba tare da ta sanya rigar mama ba.

Hotunan sun janyo mata suka da caccaka ko ta ina kafar inda wasu suka dinga zagin ta akan yadda bata dade da murmurewa daga ciwo ba ta fara shigar banza.

Wasu sun dinga yi mata wa’azi suna cewa ya kamata ta yi wa kanta fada ta daina duk wasu ayyuka marasa kyau musamman ganin ko jikin ta bata gama mayarwa ba.

A kwanakin baya jarumar ta yi ciwo wanda mutane da dama suka zaci mutuwa zata yi don duk ta rame ta fita hayyacin.

A lokacin, masoyanta sun dinga yi mata fatan alkhairi da kuma fatan zata natsu, ciwon ya zama izina a gare ta ta gyara rayuwar ta.

Ba wannan bane karon farko da jarumar ta saba yin hotuna ba tare da ta sanya rigar mama ba. Ga masu bibiyarta a Instagram, ta kan saki bidiyoyi ko kotuna sanye da riguna da suke tabbatar da hakan.

LabarunHausa.com ta tattaro wasu daga cikin tsokacin jama’a:

sir_aliyuzakeey yace:

“Allah sarki Maryam Yahaya, abin tausayi a kwanakin baya. Amma yanzu lafiya ta samu shi ne kike irin wannan shiga ko tsari, duk irin shigar nan ba shi ne wayewa ba. Allah ya shirye mu gaba daya.”

Ahmad_b_ziza yace:

“Gaskiya kina rashin mutunci. Ki yi komai ba komai, aljanna ta mai rabo ce.”

akidoashiru ya ce:

“Kafa daya a duniya daya a lahira amma an ki tuba, Allah ya rufa mana asiri.”

Hajarabellohajjo2022 ta yi tsokaci da:

“Don Allah ki dinga saka bra.”

Hachim_official yace:

“Mun gani amma ki rinka saka bireziyya.”

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe