22.5 C
Abuja
Friday, December 2, 2022

Rukayya ta shirin ‘Labarina’ tana gab da amarcewa

LabaraiKannywoodRukayya ta shirin ‘Labarina’ tana gab da amarcewa

Yayin da jaruman Kannywood suke ta tururuwar aure, wani labari mai dadi ya bayyana akan auren jaruma Fatima Isah Muhammad, wacce aka fi sani da Rukayya a shirin fim din Labarina mai dogon zango.

Kamar yadda Jaruma Umma Shehu ta wallafa wani bidiyo a shafinta na Instagram wanda ta bayyana cewa Fatima na shirin zama amarya.

rukayya l
Rukayya ta shirin ‘Labarina’ tana gab da amarcewa

Kamar yadda ta wallafa inda ta yi tsokaci, “our next couple InshaAllah “, ma’ana “ma’auratan mu na gaba InshaAllah “.

Duk da dai fuskar angon nata ba wata sananniya bace, amma muna yi musu fatan alkhairi.

Muna kuma fatan ayi auren kuma a zauna lafiya.

Ga bidiyon a kasa:

Malam Aminu Saira, ya yi karin bayani dangane da mutuwar Mahmud a shirin Labarina

Malam Aminu Saira, mai bada umarnin shirin Labarina, fim mai dogon zango ya yi karin bayani dangane da mutuwar Mahmud a shirin Labarina.

A ranar Juma’ar da ta gabata, an nuna yadda Mahmud a shirin Labarina ya mutu, wanda hakan ya sa wasu masu bin shirin su ke ganin bai yi daidai ba.

Sai dai a wata hira da VOA ta yi da Malam Aminu Saira, ya warware zare da abawa inda ya ce a fina-finai masu dogon zango, mutum ba ya gane dalilin wasu abubuwa har sai an kammala shirin.

Dangane da batun ko za a iya ganin Mahmud a ci gaban shirin fim din, Malam Aminu Saira ya ce ba zai iya bayar da amsa ba, sai dai kowa ya kwantar da hankalin sa har a kammala fim din.

Ya ce idan aka kammala shirin ala bar shi sai mutum ya gabatar da korafin sa dangane da shirin inda ya ke ganin bai dace a sa ba fim din.

A cewar sa ya kamata masu sauraro su kwantar da hankali tukunna saboda babban kalubalen da su ke fuskanta wurin shirya fim din Labarina shi ne rashin hakurin masu kallo.

Ya kuma roki jama’a da su jure, ba jan ran jama’a ake yi ba, shirya fim din ya na da matukar wahala shiyasa su ke daukar lokaci don yin shi a natse.

Ya ce a yi hukuri da yanayin shirin saboda ba za a rasa kurakurai ba, tunda ba saukakken littafi bane.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe