24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Tsoron dorinar Malam yasa na daina zuwa makarantar allo, shiyasa yanzu ban iya Larabci ba – Obasanjo

LabaraiTsoron dorinar Malam yasa na daina zuwa makarantar allo, shiyasa yanzu ban iya Larabci ba - Obasanjo

Duka na ɗaya daga cikin babban hukunci da malaman makarantar Allo ke yi a matsayin matakin gyara ga dalibai.
Da yake magana a ranar Lahadi a Abeokuta, jihar Ogun, tsohon shugaban kasa Obasanjo wanda ya yi digirin digirgir a fannin tauhidin Kiristanci, ya bayyana irin gwagwarmaya da yayi wajen neman ilimin Larabci.

Obj Olus
Tsoron dorinar Malam yasa na daina zuwa makarantar allo, shiyasa yanzu ban iya Larabci ba – Obasanjo

Ya yi jawabi ne a lokacin bikin nada Sheikh Salis Alao Adenekan a matsayin Babban Halifan Darikar Tijjaniyya na Jihohin Yarbawa, Edo da Delta.
Taron ya samu halartar shuwagabanni da kuma mambobi mabiya darikar Tijjaniyya daga dukkan jihohin Kudu maso Yamma, Edo da Delta da kuma wakilin ‘ya’yan Sheikh Ibrahim Inyass daga Kaulaha na kasar Senegal, karkashin jagorancin Sheikh Abdullah Baye Ibrahim Inyass.
Obasanjo, a takaitacciyar jawabinsa, ya bayyana cewa a matsayinsu na mabiya addini, dole ne dukkansu su yi kokari su yi aikin da zai kai su ga shiga aljanna.

Ya kara jadada cewa duk wanda yake hango aljanna a matsayin gidansa na karshe ba zai yi wasa da abinda addinin sa yakoyar ba.
Obasanjo ya ce:


“Ina mika gaisuwa ga kowa.Abin da aka tara mu a nan abu ne da ya shafi addini, Kuma daya daga cikin manyan manufofinmu, yayin da muke rayuwa a doron kasa shi ne yin aikin da zai kai mu gidan aljanna, Duk wanda ya yarda da aljanna, ba zai yi wasa da abubuwan da addini ya koyar ba a lokacin da yake raye.
“Ina gode muku da irin karamawar da aka yi wa jagoranmu, Sheikh Adenekan. Allah ya taya ka riko ya albarkaci wannan kungiya.”

Da yake magana a kan yadda ya nemi ilimin Larabci, ya ce “Lokacin da nake yaro na sha ba da labarin cewa bulaliya ita ta hanani koyon karatun Allo (Larabci) . Amma duk da haka har yanzu ina iya tuna wasu daga cikin wakokin da ake koya mana.”

Da yake gabatar da nasa bayanin,fitaccen malamin addinin musuluncin nan mazaunin Legas, Sheikh Sulaimon Faruq Onikijipa, ya gargadi masu rike da madafun iko da su guji yin amfani da mulki ba bisa ka’ida ba, yana mai cewa kar su manta za a tsaida su ranar gobe kiyama a tambayesu duk abinda suka aikata.

Onikijipa wanda shi ne Babban Shehin malamin garin Ilorin, ya kuma kalubalanci mabiya Darikar Tijjaniyya da su hada kai a matsayin kungiya domin fafutukar kare muradun al’umma tare da neman hakkinsu daga gwamnati.

A nasa jawabin, Gwamna Dapo Abiodun ya bayyana jihar Ogun a matsayin “babban birnin addini na Najeriya.”

Abiodun wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan Jihar Shu’aib Salis, ya bukaci al’ummar musulmi da su tabbatar sun sauke hakkokin dake kansu a zaben 2023 domin ganin an zabi shugabannin da za su kawo ci gaba a kasar.

Ya siffanta sabon halifan Tijjaniyya da aka nada a matsayin “Mai tsoron Allah, mutum mai daraja, rikon amana kuma jajirtaccen jakadan addinin Musulunci”.

ASUU za su yi taro yau, akwai yiwuwar ƙara wa’adin yajin aiki


Shugabannin ƙungiyar malaman jami’a ta ƙasa (ASUU) za su gudanar da taro yau Lahadi, jaridar Punch ta rahoto.

Taron zai gudana a birnin tarayya Abuja domin yin duba akan yajin aikin da ƙungiyar ke yi, a cewar ɗaya daga cikin shugabannin.

An tabbatar da taron
“Eh za mu yi taro yau a kan yajin aikin da kuma sauran wasu abubuwa”, a cewar sa.


Da aka tambaye shi ko akwai yiwuwar janye yajin aikin sai ya kada baki yace,

“Hakan da wuya, babu wani cigaba da aka samu wanda na san da shi.”


Shugaban ƙungiyar ta ASUU, Prof Emmanuel Osodeke, ya tabbatar da taron amma bai bayar da wani ƙarin bayani ba.
Taron na zuwa ne kwana ɗaya kafin ƙarewar wa’adin yajin aikin gargaɗi na wata da ASUU ta shiga.

Ƙungiyar ta ASUU a 14 ga watan Fabrairun 2022, ta bayar da sanarwar cewa ta tsunduma yajin aikin gargaɗi na sati huɗu.

Ba wani cigaba har yanzu


A wata hira da gidan talabijin na Channels Tv ranar Asabar, Osodoke ya bayyana cewa:

“Babu wani abin kirki da akayi har yanzu. Mun yi taro da ministan ƙwadago har sau biyu.

“Mun bada dama ga (NIREC) su sa baki wanda kuma sun yi. Abinda mu ka fahimta kawai shine halin nuna ko in kula da jami’o’in gwamnati
“Da ace gwamnati ta mayar da hankali da ko sati ɗaya ba ayi ba ana yajin aikin. Lokacin da aka samu matsala a ƙasar Ukraine inda ƴaƴan masu kuɗi su ke karatu, mun kalli yadda su ka saki kuɗi cikin gaggawa, amma a ƙasar da ƴaƴan talakawa su ke karatu sun kasa taɓuka komai.”

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa@gmail.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe