24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Wasu ‘yan biyu yaya da Kani sun yi wa mahaifiyarsu kisan gilla a birnin Riyadh na kasar Saudiyya

LabaraiWasu 'yan biyu yaya da Kani sun yi wa mahaifiyarsu kisan gilla a birnin Riyadh na kasar Saudiyya

Wasu ‘yan biyu da suka kashe mahaifiyarsu kuma suka ji wa babansu da wani ‘dan uwan su rauni, suna daga cikin mutane 81 wadanda aka zartarwa da hukuncin kisan da kasar Saudiyya ta yi a makon da ya gabata.. 

Yadda ‘yan biyun suka aiwatar da ta’addancin kisan


A watan Yulin shekarar 2016 ne ‘yan biyun suka ja tsohuwar mahaifiyar tasu ‘yar shekara 67 zuwa dakin ajiya inda suka dinga yankar ta da wuka babu kakkautawa a Saudiyya.


Bayan haka, sai suka koma kan Mahaifin su mai shekara 73 wanda yake a wani bangare a cikin gidan, inda shima suka caccaka masa wuka. Bayan sun gama da uban sai suka fafaro kaninsu ‘dan shekara 22 shima suka yayyanke shi da wuka. 

yanbiyu
Wasu ‘yanbiyu yaya da Kani sun yiwa mahaifiyarsu kisan gilla a birnin Riyadh na kasar Saudiyya


‘Yan biyun sun yi amfani ne da wuka mai kaifi da kuma wata zandamemiyar wuka da suka shigo da ita daga waje. Babar tasu ta mutu nan take inda aka garzaya da baban nasu da ‘dan uwan su zuwa sashen taimakon gaggawa. 


Daga baya an gano cewa, suna da alaka da kungiyar ‘yan ta’addan ISIS, wanda suke da akidar kafirta kowa, hakan ya sa suka kashe mahaifiyarsu da yunkurin kashe mahaifin su saboda sun ki yarda da waccan mummunar akida. 

Limamin masallacin Othman Almaney, yace gani na karshe da yayi wa ‘yan biyun sun shiga masallacin shi ne ranar 6 ga wata kafin faruwar lamarin. Inda shi kuma mahaifin ‘yan biyun shi ne ke fara zuwa masallacin. 

Ya kara da cewa, mahaifiyar su mutuniyar kirki ce mai girmama mutane.

Batanci ga Annabi Muhammadu SAW ya ja an yankewa Soheil hukuncin kisa 

An yankewa wani magidanci dan shekara 30 mai suna Soheil hukuncin kisa sakamakon sakonnin da yake sanyawa a shafin sa na Facebook. Sakonnin an yi su ne domin batanci ga Annabi Muhammadu (SAW ). 
Rundunar yan sandan juyin juya hali na kasar Iran wato (IRGS ) sune suka cafke Soheil din tun a watan Nuwambar shekarar 2019 tare da matarsa. 

Yana da shafuka har guda takwas a Facebook 

Arabi din yana da shafuka  wadanda aka bude da mabanbatan sunaye  har guda takwas a Facebook kuma dukkanin su ana batanci ne ga Annabi MUHAMMAD  (SAW). 
Ya kasance yana sanya abubuwa na rashin ladabi da kuma batanci ga Annabi, wanda kuma bai musa hakan ba. 
Wani dan karambani kuma dan bani na iya mai suna Eric Goldstein yace, zalunci ne a hukunta mutum domin ya sanya sako a shafin sa na Facebook, ko dan ya kalli wani abu a yanar gizo. 
Amma mai yiwuwa Eric din bai san cewa sashe na 262 na kundin doka ya bayyana karara cewa, kisa shine hukuncin duk wanda yayi batanci ko kaskantar da darajar Annabi Muhammadu (SAW ). 

Yana yada sakon batancin wasu ne kawai

Lauyan Arabi, Vahid moshkhani ya bayyana cewa kotu ta ki amincewa da kariyar da aka bashi, cewa yada sakon wadansu kawai yake yi a shafin sa, amma ba shi ne yake rubutawa ba. 
Bugu da kari, matar Soheil ta shaidawa hukumar kare hakkin dan Adam cewa, jami’an rundunar juyin juya hali ne suka kama su ita da mijin ta, a gidan su dake Tehran a watan Nuwamba.
Ta kara da cewa, daga baya sai aka saketa, amma aka ci gaba da tsare mijin ta a bangare na musamman dake kurkukun Evin. Bayan wani dan lokaci sai aka kaishi dakin kadaika, tsawon wata biyu ana yi masa tambayar titsiye. Kuma tace an hana shi ganin Lauyan sa. 
A watan Agusta na shekarar 2014 da sha hudu aka yanke masa hukuncin kisa, kuma aka dage akan haka.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@alamfas

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe