24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Makkah: Masu ibada miliyan ɗaya sun yi sallar Juma’a a masallacin Harami bayan cire takunkumin korona

LabaraiMakkah: Masu ibada miliyan ɗaya sun yi sallar Juma'a a masallacin Harami bayan cire takunkumin korona

MAKKAH: Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudi Arabiya ta tabbatar da cewa sama da mutane miliyan ɗaya ne suka gudanar da sallar Juma’a bayan cire dokar hana fita ta Covid-19.

A baya-bayan nan ne ƙasar Saudiyya ta ɗage duk wani nau’in takunkumin da ta sanya na shiga ko yin sallah a cikin masallatai masu alfarma. Hane-hane da aka ɗaga sun haɗa da nisantar da jama’a, allurar rigakafi, nuna shaidar rigakafi. Baƙi za su iya ziyarta da yin addu’a a cikin masallatai masu tsarki, Masjid al-Haram da Masjid an-Nabawi, ba tare da hani ba.

Makkah
Makkah: Masu ibada miliyan ɗaya sun yi sallar Juma’a a masallacin Harami bayan cire takunkumin korona

Bayan cire waɗannan matakan kariyar, maƙama Ibrahim (AS) ya bude wa jama’a.

Haka kuma an ware malamai a cikin babban masallacin Makkah a cikin watan Ramadan 2022 domin taimaka wa alhazai. Har ila yau, Tarawihi zai fara tare da cikakken jama’a a lokacin watan Ramadan mai zuwa.

Ma’aikatar Hajji da Umrah ta kuma tabbatar da cewa duniya za ta ga yadda aka samu karɓuwa a lokacin aikin Hajjin 2022.

Wani mutumi ya fara tattaki daga birnin London zuwa birnin Makkah inda zai shafe shekara 1 cur yana tafiya

Wani mutumi dan shekara 52, mai suna Adam Muhammed ya fara tattaki tun daga birnin London dake kasar Birtaniya, yana fatan danganawa da birnin Makka a kafa. Ya fara wannan tafiyar a watan Agustan shekarar 2021.

Tun daga lokacin da ya fara tafiyar, ya dinga dora hotunan shi a yanar gizo, inda mabiyansa suka dinga yaba masa. Mutanen da suka san shi a inda yaje, sukan bashi makwanci, abinci kuma su taimakeshi wajen tura jakarsa ta hannu, kamar yadda jaridar TRT World suka wallafa.

Adam ya kara himma wajen tattaki

Ya sami damar ratsa kasashen Netherlands, Jamus, da kuma Czech Republic. Yanzu haka, yana birnin Istanbul dake kasar Turkiyya.

Adam ya kudurci aniyar sai yaje birnin Makka a kafa, tun a watan Yuli, inda ya shirya ratsawa ta kasashen Syria da Jordan.

A hotunansa da aka yada a Instagram, an nunoshi a gaban kyanmara yanata murmushi, inda mutane da dama suka dinga yin sharhi.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe