Baturiyar da ta shafe shekaru 30 tana koyar da Hausa a Najeriya ta cika shekaru 80 a duniya

You are currently viewing Baturiyar da ta shafe shekaru 30 tana koyar da Hausa a Najeriya ta cika shekaru 80 a duniya
Baturiyar da ta shafe shekaru 30 tana koyar da Hausa a Najeriya ta cika shekaru 80 a duniya

Dan wata baturiya da ta zauna a Najeriya tsawon shekara 30 a matsayin yar mishan ya kai ta dandalin LinkedIn domin shagalin ta cika shekara tamanin 80. 


Matar mai suna Frances Boer, tayi aiki a jihar Taraba da plateau a matsayin malama a matakin ilimin farko da kuma koyar da harshen Hausa 


Danta Wiebe Boer, shi ne ya sanya hotunan ta na da tana koyarwa lokacin tana aiki a Najeriya. 

baturiya
Baturiyar da ta shafe shekaru 30 tana koyar da Hausa a Najeriya ta cika shekaru 80 a duniya

Wata mata ‘yar asalin kasar Netherlands, wadda ta zauna a Najeriya tsawon shekara 30 a matsayin ‘yar mishan, kuma malama mai koyarwa, ta cika shekara tamanin 80. 
Matar mai suna Frances Boer, ta zauna ne a Arewacin Najeriya, a matsayin malama mai koyar da harshen Hausa. 
 

Baturiya Frances Boer din ‘yar asalin kasar Netherlands ce


An haifi Frances Boer din a kasar Netherlands a lokacin yakin duniya na biyu, inda daga baya tayi kaura ta koma kasar Amrika, wanda daga can ne kuma ta dawo Najeriya. 
Da yake yada hotunan ta a kafar LinkedIn, dan ta, ya rubuta sako kamar haka:

 “Ina yi wa mahaifiya ta  Frances Boer, abar kauna murnar zagayowar ranar haihuwa. An haifeta a Netherlands lokacin yakin duniya na biyu. Sun yi kaura zuwa kasar Amurka ita da iyayen ta da kuma yayun ta guda shida, a lokacin tana ‘yar shekara 6. Bayan ta cika shekara 24 sai ta dawo Najeriya inda tayi aiki a matsayin ‘yar mishan a jihar Taraba da kuma plateau tare da baba na kimanin shekara 30. Yanzu tayi ritaya tana garin Vancouver  da ke kasar Canada “

” Lokacin da tana Najeriya, ita malama ce a matakin ilimin farko, mai koyar da Hausa ga ‘yan Najeriya , kuma mazauniyar kasashen waje.

Yadda ta iya Hausa

Dangane da yadda matar ta koyi Hausa kuwa, ga abin da  Boer din tace :

“Mahaifana sun koyi harshen Hausa a jami’ar jihar Michigan ta Amurka, shekara daya kafin su koma Najeriya a shekarar 1966, inda suka share shekaru 10 a Wukari da Baissa dake jihar Taraba, wanda a nan ne suke magana da harshen Hausa har suka goge sosai. A shekarar 1980 babata tana iya koyar da harshen Hausar, inda shi kuma babana yake rubuce-rubucen littattafai da harshen na Hausa


Bayan Boer ya yada Labarin, mutane da dama sun nuna sha’awar su a kai, inda suka fara fadar ra’ayin su.


Ga kadan daga ciki :  


Sylvester Oluoha yace :

” wannan yayi kyau Wiebe Boer PhD, na san dole ne ta baka sunan hausawa Menene sunan ka na hausawa? “


Christabel Bentu cewa yayi:

” Murnar karin shekara ga mama… Mun gode Allah da dunbin shekarun da kika shafe, muna miki fatan wasu masu yawa a gaba…Mun gode miki da zaman ki  a plateau akan hidimar addini.”

Daga zuwa Najeriya sauro ya cijeta, sai da likitoci yi wa baturiya aiki 36 tare da yanke mata kafafunta 2

Wata mata baturiya ‘yar kasar Australia ta bayyana yadda likitoci su ka yi mata aiki 36 sannan su ka yan ke mata kafafunta guda biyu bayan ta kamu da ciwon Malaria bayan kai ziyara jihar Legas da ke Najeriya.
Matar mai shekaru 52 ta kai ziyarar kasuwanci jihar Legas a shekarar 2019 bayan wata gayyata da aka yi mata.
Yayin tattaunawa da Sydney Morning Herald, ta ce yayin taron, an bukaci ta dauki hoto gefen wani ruwa mara gudana daga nan sauraye guda uku su ka cijeta kafarta ta hagu.

Bayan komawa Kasar Indiya da kwanaki, sai ta fara fama da kasala, daga nan aka wuce da ita asibiti a lokacin dakyar ta ke cin abinci. A nan ne aka tabbatar da cewa ta kamu da ciwon Malaria.
Daga nan likitoci su ka ce ciwonta ya yi tsanani don Malaria ta yi mata mugun kamu, daga nan aka ba ta magunguna.
Jini ya daina gudana ta wasu bangarori da ke jikinta a lokacin aka sanar da ‘yan uwanta cewa matsawar ta rayu akwai bangarorin da za su daina aiki a jikinta.
Sakamakon magungunan da ta sha kafarta ta samu matsala har sai da aka yanke. Ana yi mata aiki lafiyarta na kara tabarbarewa don haka sai da aka yanke kafafunta biyu.
Ta fuskanci ciwo mai radadi don ko zama a kujerar guragu azaba ce a wurinta, daga baya aka hada mata kafafun karfe wadanda take tafiya da su yanzu haka.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]

Rubuta Sharhi