Ina tsoron ranar haduwa ta da Allah, cewar Taver Tersugh matashi da ya mayar da makudan kudin da aka yi kuskuren tura masa

  • Post author:
  • Reading time:5 mins read
You are currently viewing Ina tsoron ranar haduwa ta da Allah, cewar Taver Tersugh matashi da ya mayar da makudan kudin da aka yi kuskuren tura masa
Ina tsoron ranar haduwa ta da Allah, cewar Taver Tersugh matashi da ya mayar da makudan kudin da aka yi kuskuren tura masa

Irin yadda gaskiya da Amana ta yi karanci ba kasafai ba ne matashi zai maida abunda ba na shi ba. Wani dan Najeriya mai suna Taver Tersugh James ya mayar da kudi naira 10,000 da wani ma’aikacin POS ya tura mishi a bisa kuskure. Lamarin ya faru ne a Makurdi, babban birnin jihar Benuwai.

Wani bayani da Legit.ng ta samu ya nuna cewa ana shirin tuhumar mai aiki a POS din kenan a daidai lokacin da Taver Tersugh ya yanke shawarar mayar da kudin.

Fushi
Ina tsoron ranar haduwa ta da Allah, cewar Taver Tersugh saurayin da ya mayar da makudan kudin da aka yi kuskuren tura masa

Abokai sun bani shawarar kar in mayar da kudin

Matashi Taver ya ce wasu abokansa sun gaya masa cewa kudin da aka turo masa Allah ne ya ciyar da shi. Ya ce sun ba shi shawarar kada ya mayar.
Duk da haka, bai yadda yadauki shawarar su ba maimakon haka sai ya yanke shawarar kai kuɗin ga wakilin POS din. Ga sakon da aka aika wa Legit.ng in da yake cewa:

Wani matashi mara aikin yi a jihar Benuwe mai suna Taver Tersugh James ya mayarwa ma’aikacin POS da ke Makurdi babban birnin jihar Benuwe kudi 10,000 da aka turo masa ba bisa ka’ida ba.

“Ya bayyana cewa a koda yaushe yana sha’awar zama sanadiyar alheri ga wani amma ba tsiya ba wanda zai iya janyo fushin Ubangiji. Ya kara da cewa wasu daga cikin abokan sa sun ba shi shawarar da kada ya mayar da kudin inda suka jaddada masa cewar wannan wata hanya ce da Ubangiji ya ciyar da shi amma sai yaki bin maganar su, suma kuma ya ya musu nasiha a kan wannan mummunar dabi’a domin samun cigaba a cikin al’umma.

Rayuwa ta yi tsadda amma haka ya daure ya mai da kudin ga mai su

Duba da irin yadda Rayuwa ta yi tsada, ya kara da cewa amma na san Allah zai kawo sauki. Wakiliyyar POS wanda maigidan ta ya yi barazanar zabtare kudin daga cikin albashin ta, ta bayyana matashin a matsayin mutum mai kyakywan niyya ga al’umma.

Matashin da ya bar makaranta ya kera motoci masu amfani da wutar lantarki a Maiduguri

Wani lamari mai girman gaske yana faruwa a Maiduguri, babban birnin jihar Borno. Wani matashi ɗan shekaru 29 mai suna Mustapha Gajibo yana ƙera motoci da keke mai kafa uku masu amfani da wutar lantarki sannan yana sauya fasalin injinan motoci

Matashin ya bar jami’a

Abin mamaki shine Gajibo ya bar makaranta. Ya bar jami’ar Maiduguri a shekarar 2015 bayan yakai shekara ta uku. Ya bar makarantar ne saboda an bashi General Agriculture a maimakon Electrical Engineering wanda yake matuƙar so.

Da yake magana da Legit.ng, matashin ya bayyana cewa motocin na sa a nan ƙasar ake ƙera su. Motar za ta iya tafiyar tsawon kilomita 100 zuwa 150 kafin ta buƙaci ayi mata caji.

Ga abinda yake cewa:

Eh komai da komai ana yin sa ne anan birnin Maiduguri na jihar Borno. Ina alfahari da cewa dukkan ma’aikatan da mu ke aiki da su akan wannan shirin an samo su ne sannan aka ba su horo anan gida Najeriya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Rubuta Sharhi