Abubuwan da ke ciki
Shugabannin ƙungiyar malaman jami’a ta ƙasa (ASUU) za su gudanar da taro yau Lahadi, jaridar Punch ta rahoto.
Taron zai gudana a birnin tarayya Abuja domin yin duba akan yajin aikin da ƙungiyar ke yi, a cewar ɗaya daga cikin shugabannin.
An tabbatar da taron
Eh za mu yi taro yau akan yajin aikin da kuma sauran wasu abubuwa.
A cewar sa
Da aka tambaye shi ko akwai yiwuwar janye yajin aikin sai ya kada baki yace,
Hakan da wuya, babu wani cigaba da aka samu wanda na san da shi.
Shugaban ƙungiyar ta ASUU, Prof Emmanuel Osodeke, ya tabbatar da taron amma bai bayar da wani ƙarin bayani ba.

Taron na zuwa ne kwana ɗaya kafin ƙarewar wa’adin yajin aikin gargaɗi na wata da ASUU ta shiga.
Ƙungiyar ta ASUU a 14 ga watan Fabrairun 2022, ta bayar da sanarwar cewa ta tsunduma yajin aikin gargaɗi na sati huɗu.
Ba wani cigaba har yanzu
A wata hira da gidan talabijin na Channels Tv ranar Asabar, Osodoke ya bayyana cewa:
Babu wani abin kirki da akayi har yanzu. Mun yi taro da ministan ƙwadago har sau biyu.
Mun bada dama ga (NIREC) su sa baki wanda kuma sun yi. Abinda mu ka fahimta kawai shine halin nuna ko in kula da jami’o’in gwamnati
Da ace gwamnati ta mayar da hankali da ko sati ɗaya ba ayi ba ana yajin aikin. Lokacin da aka samu matsala a ƙasar Ukraine inda ƴaƴan masu kuɗi su ke karatu, mun kalli yadda su ka saki kuɗi cikin gaggawa, amma a ƙasar da ƴaƴan talakawa su ke karatu sun kasa taɓuka komai.
Gwamnatin tarayya ba ta da kudin da zata iya biyan ASUU -inji ministan Buhari
Ministan ƙwadago Dr Chris Ngige ya bayyana cewa gwamnatin tarayya bata da kuɗaɗen da zata iya cika alƙawarin da ta yiwa ƙungiyar malama jami’a ta ƙasa watau ASUU.
Ngige ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na duba yiwuwar sake tattauna alƙawarin da ke tsakanin ta ASUU domin ganin an kawo ƙarshen yajin aikin da malaman jami’ar ke yi. Jaridar PUNCH ta rahoto
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com