Yadda budurwa ta bar saurayinta bayan ya sama mata aiki sannan ya ranci kudi don shirya mata bikin ‘birthday’

  • Post author:
  • Reading time:5 mins read
You are currently viewing Yadda budurwa ta bar saurayinta bayan ya sama mata aiki sannan ya ranci kudi don shirya mata bikin ‘birthday’
Yadda budurwa ta bar saurayinta bayan ya sama mata aiki sannan ya ranci kudi don shirya mata bikin ‘birthday’

Wata budurwa ta bar saurayin ta bayan ya tallafa wa rayuwarta kuma ya yi mata halacci a rayuwa.

An samu bayanai kamar yadda shafin Instablog9ja ta wallafa a Facebook akan wani saurayi da budurwarsa.

chat
Yadda budurwa ta bar saurayinta bayan ya sama mata aiki sannan ya ranci kudi don shirya mata bikin ‘birthday’

Abokin saurayin, wani Michael, mai amfani da @michael_mickyt ne ya wallafa a shafinsa na Twitter inda ya shaida irin cin amanar da aka yi wa abokinsa.

Kamar yadda ya shaida a wallafa:

“An yaudari daya daga cikin abokai na, duk da ya tallafa wurin samar wa budurwarsa aiki wanda tsawon shekaru tana nema ba tare da ta samu ba.

“Bayan wata daya tana aikin ta hadu da wani wanda ta fara soyayya da shi.

“Abunda ya fi bata min rai shi ne yadda ya ranci kudi duk don shirya mata bikin zagayowar ranar haihuwar ta duk saboda soyayya.

“Dama ta tsaya ta biya bashin da ake bin shi kafin ta rabu da shi.

“Abin lura shi ne, yanzu haka sabon saurayin nata a wurin da ta samu aiki yake yin aiki.”

Budurwa ta maka Fasto a kotu kan yaudarar ta da yayi ta hanyar yi mata alkawarin aure

A kan alkawarin aure Kwanye Tumba, ta kai faston House of Chapel dake Karewa, karamar hukumar Yola ta arewa dake jihar, zuwa kotun masu laifi mai daraja ta II.

Kwanye ta bayyana wa Honourable Nuhu Musa, alkalin kotun, cewa wani fasto mai shekaru 28, Marwa Tumba, ya yi mata alkawarin aure amma ya tsere ya koma wurin wata budurwar bayan ya gama lalube mata ‘yan kudadenta.

Ta bayyana wa kotu yadda suka fara haduwa a wata coci dake Yolde Pate, wani bangare na karamar hukamar Yola ta kudu a 2019, inda yace mata ya duba ya ga har ta samu miji.

A cewarta, Fasto Marwa ya sanar mata da cewa yanzu haka ta zama matarsa, don haka ta fara shuka tun yanzu.

Ta bukaci yayi mata bayani akan shukar da za ta fara, sai yace ta bashi N1,000.
Ta ce tun daganan yake zuwa gidanta wanda ta gina lokacin tana aiki da wata NGO, inda take tarbarsa ta yi masa girki da sauransu, daga nan suka fara soyayya yayi mata alkawarin aure.

Ta bayyana yadda faston ya sa ta bar aikinta kuma ta siyar da gidanta N500,000. A cewarta, bayan an biya ta kudin gidan ta tura masa N50,000, kuma tayi amfani da sauran kudin wurin tallafa wa coci har suka kare.

Ta ce akwai lokacin da ya bukaci ta gabatar masa da duk abubuwan da ake bukata na aure kamar yadda al’ada ta samar, kuma tayi hakan. Sannan ta koma wurin iyayenta a Machika don jiransa, bayan ya yi alkawarin zuwa don su yi aure.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Rubuta Sharhi