Matsalar tsaron Najeriya ta gyaru, Boss Mustapha

  • Post author:
  • Reading time:5 mins read
You are currently viewing Matsalar tsaron Najeriya ta gyaru, Boss Mustapha
Matsalar tsaron Najeriya ta gyaru, Boss Mustapha
  • Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya ce yanzu haka matsalar tsaron Najeriya ta gyaru
  • Ya bayyana hakan ne yayin jawabi a wani taro da aka yi a garin Kaduna ranar Alhamis, 10 ga watan Maris
  • A cewarsa, rashin tsaron arewa maso gabas da yunkurin raba kasar da kudu maso gabas take yi ya ragu

Sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Boss Mustapha, ya ce matsalar rashin tsaron da ke Najeriya ya gyaru sosai, Instablog9ja.com ta ruwaito.

Yayin jawabi a wani taro da aka yi a garin Kaduna ranar Alhamis, 10 ga watan Maris, Mustapha ya ce matsalar rashin tsaron da ya yi katutu a arewa maso gabas da kuma barazanar raba kasa da kudu maso gabas suke ta yi a baya duk sun ragu.

boss mustapha
Matsalar tsaron Najeriya ta gyaru, Boss Mustapha

A cewarsa, yanzu haka ‘yan ta’adda da dama mika wuya tare da tuba daga munanan ayyukan su.

Mustapha ya ce:

“Rashin tsaro ya gyaru kwarai a fadin kasar nan. Barazanar rana kasa da kudu maso gabas da kuma wani yanki na kudu-kudu suke yi ya ragu kwarai.

“Mun samu kwanciyar hankali don mun dade bamu samu rahoto akan ‘yan ta’adda sun kai farmaki wani wuri ba.

“Rundunar Operation Sharan Daji tare da taimakon jami’an rundunar ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro na sirri sun taimaka wurin ganin bayan ‘yan ta’adda.”

Yadda za a magance matsalar tsaro a Najeriya -Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya roƙi gwamnatin tarayya ta magance matsalolin tsaro, rashin aikin yi, talauci, cin hanci da rashawa, lalacewar muhalli da shigowar makamai domin kawo ƙarshen matsalolin tsaro.

Ya bayyana hakan ne a yayin wata lakca da ya gabatar a jami’ar Ibadan. Jaridar Daily Trust ta rahoto

Hanyoyin magance matsalolin tsaro

Ganduje ya bayyana cewa ƙirƙiro da kuma tabbatar da aiwatar da manufofi, tare da shirye-shiryen da za su kawo ƙarshen matsalolin tsaro na da matuƙar muhimmanci.  

A Najeriya, ana yin ƙulla-ƙulla a laifukan da su ka shafi matsalolin tsaro.  Hakan ya sanya doka ba ta tsawatar wa.

Hukumomin tsaron mu dole ne su daina amsar cin hanci. Domin tabbatar da hakan dole ne a samar da yanayi mai kyau na gudanar da aiki, da kuma samar da walwala.  

Ganduje ya yaba da wata sabuwar doka

Ya ƙara da cewa dokar da aka kawo ta kwana-kwanan nan da ta mayar da garkuwa da mutane a matsayin aikin ta’addanci a matsayin abinda ya dace.

Najeriya ta na fama da matsalolin tsaro waɗanda su ka daɗe suna addabar ƙasar.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]

Rubuta Sharhi