Zaɓen 2023: Gwamnoni sun fusata, sun cimma wata babbar matsaya akan takarar shugabancin ƙasa

  • Post author:
  • Reading time:5 mins read
You are currently viewing Zaɓen 2023: Gwamnoni sun fusata, sun cimma wata babbar matsaya akan takarar shugabancin ƙasa

Gwamnoni 36 na jihohin ƙasar nan sun cimma matsayar cewa lallai shugaban ƙasar nan na gaba ya fito daga cikin su.

Gwamnonin kamar yadda aka nuna sun dage kan cewa lallai sai sun samar da shugaban ƙasa na gaba idan shekarar 2023 ta ƙaraso. Jaridar Independent.ng ta rahoto

Sun amince da matsaya ɗaya

Wata majiya a ƙungiyar gwamnonin Najeriya wacce ta bayyana hakan a ƙarshen mako, ta ƙara da cewa dukkanin gwamnonin daga jam’iyyun APC da PDP sun gama shirin cewa ɗan takarar shugaban ƙasa ya fito daga cikin su.

Majiyar ta kuma ƙara da cewa dukkanin gwamnonin 36 sun cimma matsayar cewa ɗaya daga cikin su ba tare da yin la’akari da jam’iyyar da ya fito shine zai zama shugaban ƙasa na gaba. 

Gwamnonin za su marawa duk jam’iyyar da fitar da ɗan takaranta daga cikin su, idan har wata jam’iyyar ba ta fitar da ɗan takaranta daga cikin su ba. 

Majiyar ta bayyana cewa:

Ina faɗa maka cewa gwamnonin jihohi 36 sun cimma matsaya kan cewa ɗaya daga cikin su ya zama shugaban ƙasa na gaba a ƙasar nan.

Gwamnonin sun yi tarurruka da dama akan wannan lamarin inda har sun yi nisa sosai. A cikin kwanaki kadan masu zuwa za su fitar da sanarwa akan wannan ƙudirin.

Sun dage akan ƙudirin su

An kuma ƙara samo cewa wannan shine babban maƙasuɗin da ya sanya gwamnonin jam’iyyar APC su ƙa dage wajen amshe ragamar kwamitin riƙon kwarya da shirya babban taron jam’iyyar kafin zuwan taron jagororin jam’iyyar na ƙasa ranar Alhamis, a shirye-shiryen da ake na babban taron jam’iyyar mai zuwa cikin wannan watan.

A jam’iyyar PDP, su ma gwamnonin ba su yi ƙasa a guiwa ba wajen cigaba da ƙara kaimi wajen neman shawarwari a wajen shugabannin jam’iyya kafin zuwan babban taron ƙusoshin jam’iyyar ranar Litinin a birnin tarayya Abuja da kuma taron jagororin jam’iyyar ranar Talata.

Zaɓen 2023: Dole ne shugaban ƙasa ya fito daga kudancin Najeriya -wata ƙungiya ta magantu

Wata ƙungiya mai suna Defense for Yoruba People’s Rights, tayi kira da jam’iyyun Peoples Democratic Party (PDP) All Progressives Congress (APC) da sauran jam’iyyu kan cewa su zaɓo ɗan takarar shugaban ƙasa a zaben 2023 daga yankin kudancin Najeriya.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Otunba Muyideen Olamoyegun, ya fitar a birnin Akure, na jihar Ondo ranar Talata. Jaridar Punch ta rahoto

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Rubuta Sharhi