22.9 C
Abuja
Friday, December 2, 2022

Yadda na hadu da dirarriyar mata ta daga yin tsokaci karkashin wata wallafar Facebook

LabaraiYadda na hadu da dirarriyar mata ta daga yin tsokaci karkashin wata wallafar Facebook
  • Wani matashi, Olayede Godwin, ya labarta yadda kafar sada zumuntar zamani ta taimaka mishi wurin samun matar da ya aura
  • Hirar ma’auratan ta farko ta fara ne a bangaren tsokacin wallafar Legit.ng na Facebook, inda suka fara hirarraki
  • Basu kai shekara da sanin juna ba, masoyan suka karfafa soyayyar su, sannan sukayi aure a watan Maris din shekarar 2022

Wani dan Najeriya, a wani sako da ya tura wa Legit.ng ya bayyana yadda ya hadu da matarsa, Talatu Precious Mohammed Akoa.

Oloyede ya bayar da labarin yadda ya hadu da matarsa a sashin tsokaci na Facebook, karkashin wallafar da Legit.ng tayi.

tsaleliyar mata da miji
Yadda na hadu da dirarriyar mata ta daga yin tsokaci karkashin wata wallafar Facebook

Ya kara da bayar da labarin yadda a wurin tsokacin ne suka fara magana. Mata da mijin sun hadu karkashin wallafa a Facebook.

“Mun hadu, gami da yin aure bayan watanni uku,” kamar yadda ya shaida.

Kaddara ta hada su a wajen shagalin biki. Inda a nan ne suka yimusayar Lamba.

Haka zalika, matashin ya turo da tsala-tsalan hotunan da suka dauka kafin aure.

Wani bangare daga cikin sakon sa na nuna:

“A zahirin gaskiya, mun hadu a Facebook ne, kuma hirar mu ta farko akan wata wallafa da kuka yi ce.

“Bazan iya tunawa da wallafar ba. Bayan watanni uku muka hadu a wani biki, inda muka yi musayar lamba…”

BASAJAN AIKI: Bayan wata uku 3, wata mata ta gano ‘yar aikin da ta dauka ba mace bace, gardi ne 

Wata mata ‘yar Nageriyar ta dauki wata ‘yar aiki, bayan wata uku sai ta gane ashe burum-burum ‘yar aikin tayi mata. 
Matar ta gano cewa ‘yar aikin dai ba mace bace namiji ne inda ta kunyata shi a cikin bidiyon da ya dinga kewayawa a kafafen sada zumuntar zamani.

Anyi ta samun ra’ayoyi mabanbanta juna lokacin da bidiyon dan basajan aikin ya yadu, inda mutumin ya zamo abin ya taba shi sosai. 

Kaddara cewa ku dauki yar aiki mace, bayan wani lokaci kuma ku gano cewa wannan ‘yar aikin ba mace bace namiji ne. Wannan shi ne abin da ya faru da wata magidanciya. 

Matar wacce babu wani takamaiman bayani a kan wacece ita, ta ga abinda ta kasa yarda da shi, cewa mai aikin gidanta ba mace bace namiji ne. 

Lamarin wanda @ourtalkroom ne ya yada bidiyon sa, yace matar ba ta gane cewa ‘yar aikin ba mace bace namiji ne, sai bayan watanni uku. 

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe