22.5 C
Abuja
Friday, December 2, 2022

Talaka aka bari yana hauka: Hotunan Atiku da Osinbajo sun kebe suna zantawa a wata liyafa

LabaraiTalaka aka bari yana hauka: Hotunan Atiku da Osinbajo sun kebe suna zantawa a wata liyafa
  • Atiku Abubakar na daya daga cikin bakin da suka halarci bikin nadin sarautar sabon Olubadan, Lekan Balogun da akayi a ranar Juma’a, 11 ga watan Maris
  • Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo da wasu yan majalisar jihar ma sun samu damar halartar kasaitaccen taron
  • Inda gwamna Seyi Makinde da takwaransa na jihar Ogun, Dapo Abiodun, dan takarar shugaban kasa a Jam’iyyar PDP aka gansu a wasu hotuna da aka wallafa a ranar Juma’a suna zantawa a gefe guda da Osinbajo, Makinde da Aboidun

Jiga-jigai da dama sun halarci nadin sarautar Lekan Balogun a matsayin Olubadan na 42 a kasar Ibadan cikin jihar Oyo a ranar Juma’a, 11 ga watan Maris, Legit.ng ta ruwaito.

Daga cikin hamshakan yan siyasar Najeriyan da suka dabbaka taron ta hanyar talarta sun hada da; tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, Maitamakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun, tsoffi da gwamnoni masu ci.

Talaka aka bari yana hauka: Hotunan Atiku da Osinbajo sun kebe suna zantawa a wata liyafa
Talaka aka bari yana hauka: Hotunan Atiku da Osinbajo sun kebe suna zantawa a wata liyafa

A kafar sada zumuntar Twitter, Atiku ya wallafa hotunan da ke nuna lokuta a taron, daga ciki har da takaitacciyar hirar su da Osinbajo da gwamna Abiodun.
Haka zalika, anga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP na zantawa da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde.

Atiku yayi wallafa a Twitter game da taron: “HRH Oba Lekan Balogun, Olubadan na 42 a kasar Ibadan, Ubangiji ya ja zamanin ka cikin basira da kwanciyar hankali.”

Da farko dai, gwamnan jihar Oyo ne ya nada Balogun a matsayin Olubadan na 42 a kasar Ibadan a ranar Juma’a.

Makinde ya gabatar wa basaraken ofishin ne a kasaitaccen taron da akayi a ranar Juma’a a dakin taron Mapo cikin garin Ibadan. A kalamanshi bayan an nadashi a matsayin Olubadan, Balogun ya lashi takobin cewa bazai bawa mutanen kasar Ibadan da kasar baki daya kunya ba.

A cewarsa, “Inaso in ba kowa tabbacin cewa bazan kunyata mutanen Ibadan ba. Kuma bazan bawa mutanen Najeriya kunya ba.”

Sabon basaraken ya bayyana godiyarsa ga masu nada sarakuna, tsoffin da yan majalisar jihar, akan yadda suka girmama gayyatar shi. Daga cikin jiga-jigan da suka halarci taron sun hada da ; Atiku Abubakar, Aboidun, Gwamna Kayode Feyemi, Lamidi Adeyemi, Alaafin na Oyo; Adeyeye Ogunwusi, Oonin Ife; Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar.

Magoya bayan Atiku sun juya masa baya, sun ce yayi tsufa da kujerar shugaban kasa

Kungiyoyin sun zaburo akan bukatar mayar da mulki kudu da kuma bukatar samar da shugaban kasa mai karancin shekaru a 2023 ta bukaci tsohon shugaban kasa, Atiku Abubakar ya dakatar da burin sa ba tsayawa takara, The Guardian ta ruwaito.

Cikin kungiyar akwai manyan shugabannin da ke yi wa Atiku kamfen kamar shugaban kungiyar Turaki Arewa Vanguard na kasa, shugaban kungiyar Middle Belt Network for Atiku; shugaban kungiyar Atiku 2023 ta kudu maso yanma da kuma shugaban kungiyar North4North Support Group for Atiku.

Shugaban kungiyoyin, Femi Osabinu ya bijiro da wannan bukatar ne a wani kwarya-kwaryan taro na manema labarai wanda aka yi a cibiyar kungiyar manema labarai, NUJ da ke Abuja a jiya, inda ya ce Najeriya tana bukatar matashi mai jini a jika don ya samu kuzarin da zai iya tafiyar da mulki.

Kamar yadda yace:

“Duk da Atiku ya yi wa kasa aiki da kyau wanda hakan yasa muke goya masa baya tsawon shekaru, amma maganar gaskiya shekarar sa 77, bai dace ya shiga takara ba. Duk wanda ya kalli halin da kasa take ciki ya kamata ya yi nazari.

“Najeriya tana bukatar matashi mai jini a jika, wanda zai iya jajircewa wurin ganin ya kawo mafita ga kasa da kuma yin ayyukan sa a matsayin sa na shugaba ba tare da gazawa ba.

“A shekarar 2007, lokacin da tsohon shugaban kasa Obasanjo yake kokarin yin mulki a karo a uku, Atiku ne ya zaburo ya ce ya kamata mulki ya koma arewa.”

Ya kara da cewa, ganin irin gwagwarmayar da Atiku ya yi a bangarori daban-daban na gwamnati har ya rike kujerar mataimakin shugaban kasa har ya iya yin ayyuka yadda ya dace babban abin dubawa ne.

Amma a cewarsa, lokaci ya yi da Atiku zai koma baya, ya zama mai bayar da shawarwari dangane da harkokin shugabanci a Najeriya don su ne dattawan kasa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe