2023: PDP ce za ta samar da shugaban ƙasar Najeriya, Obaseki

You are currently viewing 2023: PDP ce za ta samar da shugaban ƙasar Najeriya, Obaseki
2023: PDP ce za ta samar da shugaban ƙasar Najeriya, Obaseki

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya bayyana yakinin sa akan cewa shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Sanata Iyorchia Ayu, zai mayar da jam’iyyar kan karagar mulki a shekarar 2023, The Punch ta ruwaito.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ya yi alkawarin yin aiki da shugabannin jam’iyyar don ganin jam’iyyar PDP ta samar da shugaban ƙasar a zabe mai zuwa.

2023: PDP ce za ta samar da shugaban ƙasar Najeriya, Obaseki
2023: PDP ce za ta samar da shugaban ƙasar Najeriya, Obaseki

Obaseki ya bayyana haka ne a wajen wata liyafar cin abincin dare da aka yi wa shugaban na ƙasa a gidan gwamnati da ke birnin Benin, babban birnin jihar Edo.

Gwamnan ya ce, “Mun yi farin cikin zuwan ku Edo kuma mun gode muku da nuna soyayya. Ba za mu je ko’ina ba; muna nan don taimaka muku wurin ciyar da PDP gaba.

“Mun san ƙalubalen da kuke fuskanta. Amince da mu, muna nan don tallafa muku kuma za mu kasance tare da ku. Da yardar Ubangiji za ku yi nasara wajen fitar da shugaban kasarmu mai girma.”

Obaseki ya ce, “Abin da ya gabata ya wuce, mu mayar da hankali kan gaba. Kun bayyana mana yadda kuka shiga wajen kafa wannan jam’iyya. Siyasar da muka yi a 1999 ba za ta kasance a yanzu ba. Fasahar da ke cikin 1999 ba ta da dacewa kamar fasahar yau.”

“A shekarar 1999, tunanin duniya baki daya ya dogara ne da albarkatun ma’adinai, amma a yau, duniya ta dogara da ƙarfin dan Adam da fasaha ne. Duniya ce ta daban kuma Edo ce ke jagorantar canjin siyasar mu, ”in ji shi

A nasa ɓangaren, Ayu ya yabawa Gwamnan bisa ci gaban da yake samu a dukkanin sassan jihar, inda ya yaba masa bisa nasarorin da aka samu a cikin rajistar shafukan yanar gizo na jam’iyyar PDP na jihar.

Jerin jihohin da jam’iyyar APC ke da iko da su, da kuma jihohin da PDP ke da iko da su

Bayan canja shekar gwamna Matawalle, zuwa jam’iyya APC zamu kawo muku jerin jihohin da manyan jam’iyyun siyasar kasar nan suke da iko da su.

Bayan shafe watanni ana ta faman tataburza akan canja shekar shi, a karshe dai gwamna Bello Matawalle ya koma jam’iyyar APC mai mulki, a ranar 29 ga watan Yunin shekarar 2021.

Ya zuwa yanzu dai jam’iyyar APC ta samu karuwar gwamnoni guda uku wadanda suka canja sheka daga jam’iyyar PDP suka dawo cikinta, yayin da babban zabe na 2023 ke karato wa.

Gwamnonin su ne:

  1. Gwamna David Umahi (Ebonyi))
  2. Gwamna Ben Ayade (Cross River)
  3. Gwamna Bello Matawalle (Zamfara)

Bayan kammala zaben gwamnoni guda biyu na jihar Edo da Ondo a shekarar 2020, babbbar jam’iyya mai mulki na rike da jihohi 20, inda babbar jam’iyyar adawa kuma take rike dda jihohi 14. Sauran jihohin sunaa hannun jam’iyyar APGA.

Sai dai kuma sakamakon canje-canje da aka samu, musamman ma a yanzu a jam’iyyar PDP da aka samu wanda suka fita daga cikinta, wannan kididdiga ta canja.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

SourceLegit.ng

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Rubuta Sharhi