Yadda za a magance matsalar tsaro a Najeriya -Ganduje

  • Post author:
  • Reading time:4 mins read
You are currently viewing Yadda za a magance matsalar tsaro a Najeriya -Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya roƙi gwamnatin tarayya ta magance matsalolin tsaro, rashin aikin yi, talauci, cin hanci da rashawa, lalacewar muhalli da shigowar makamai domin kawo ƙarshen matsalolin tsaro.

Ya bayyana hakan ne a yayin wata lakca da ya gabatar a jami’ar Ibadan. Jaridar Daily Trust ta rahoto

Hanyoyin magance matsalolin tsaro

Ganduje ya bayyana cewa ƙirƙiro da kuma tabbatar da aiwatar da manufofi, tare da shirye-shiryen da za su kawo ƙarshen matsalolin tsaro na da matuƙar muhimmanci.  

A Najeriya, ana yin ƙulla-ƙulla a laifukan da su ka shafi matsalolin tsaro.  Hakan ya sanya doka ba ta tsawatar wa.

Hukumomin tsaron mu dole ne su daina amsar cin hanci. Domin tabbatar da hakan dole ne a samar da yanayi mai kyau na gudanar da aiki, da kuma samar da walwala.  

Ganduje ya yaba da wata sabuwar doka

Ya ƙara da cewa dokar da aka kawo ta kwana-kwanan nan da ta mayar da garkuwa da mutane a matsayin aikin ta’addanci a matsayin abinda ya dace.

Najeriya ta na fama da matsalolin tsaro waɗanda su ka daɗe suna addabar ƙasar.

Ganduje ya naɗa Aliko Dangote, Dantata da Abdulsamad Rabiu wani babban muƙami a jihar Kano

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, a ranar Laraba ya naɗa attajirin da  yafi kowa arziƙi a nahiyar Afrika, Aliko Dangote, kawun sa Aminu Ɗantata, da Abdulsamad Rabi’u a matsayin mambobin hukumar Zakka da Hubsi ta jihar.

Naɗin ya biyo bayan amincewar da majalisar gudanarwar jihar ta yi na sake fasalin hukumar Zakka da Hubsi ta jihar wacce Dr Ibrahim Mu’azzam Maibushira ya samu ragamar jagoranta. Jaridar Independent.ng ta rahoto

A wata sanarwa da kwamishinan watsa labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ya fitar, ya lissafo Dr AbdulMutallab Ahmed a matsayin kwamishina na ɗaya da Dr Lawi Sheikh Atiq a matsayin kwamishina na biyu na hukumar.

A cewar sa, sauran mambobin hukumar sun haɗa da wakilai daga masarautun jihar guda biyar, wakilai daga ministirin watsa labarai da ministirin harkokin addini, wakilai daga kasuwannin  Kurmi, Rimi Kwari da Singer

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]

Rubuta Sharhi