Wani ɗan majalisa ya bayyana gaskiya dangane da takarar Osinbajo

  • Post author:
  • Reading time:5 mins read
You are currently viewing Wani ɗan majalisa ya bayyana gaskiya dangane da takarar Osinbajo

Ɗan majalisa mai wakiltar Osun ta yamma, Sanata Adelere Oriolowo, ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Legas kuma jagoran APC  na ƙasa Asiwaju Bola Tinubu, yana da koshin lafiya da kuzarin da zai iya zama shugaban ƙasar Najeriya.

Sai dai Oriolowo, yayi watsi da muradin mataimakin shugaban ƙasa Prof Yemi Osinbajo, a matsayin jita-jita ce kawai. Inda ya ke cewa Tinubu ne kawai ɗan takarar shugaban ƙasa da su ka sani daga jam’iyyar APC a yankin kudu maso yamma.

Ɗan majalisar ya bayyana hakan ne ranar Juma’a a birnin tarayya Abuja yayin da ya ke ganawa da ‘yan jarida.

Tunibu na da cikakkiyar ƙoshin lafiya

Da ya ke mayar da martani dangane da maganganun da ake yaɗawa kan cewa Tinubu ya tsufa kuma bai da lafiyar da zai iya shugabancin Najeriya a 2023, Oriolowo ya bayyana cewa Tinubu yana da lafiyar da zai iya tafiyar da mulkin Najeriya domin kai ta ga mataki na gaba.

Ɗan majalisar ya bayyana cewa Tinubu zai tsaya takara a zaɓe mai zuwa, inda ya jaddada cewa kiran da ake yi na bayar da takara ga ‘yan ƙabilar Ibo bai zai hana shi cika muraɗin sa ba.

Tinubu bai tsoron takarar Osinbajo

Da aka tambaye shi ko cewa neman takarar da Prof Yemi Osinbajo ya ke yi ko za ta iya kawo wa Tinubu cikas a neman takarar sa, ɗan majalisar yayi watsi da takarar mataimakin shugaban ƙasar a matsayin jita-jita ce kawai.

Osinbajo
Mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo

Oriolowa ya bayyana cewa:

Bana yin aiki akan jita-jita. Neman takarar Yemi Osinbajo jita-jita ce kawai a wajen mu ‘yan jam’iyyar APC na yankin kudu maso yamma. Bai faɗawa kowa cewa yana son tsayawa takara ba sannan ba wani abu da ya nuna cewa zai tsaya takara. Mu bar zancen kawai a matsayin jita-jita.

Ɗan majalisar kuma ya tabbatar wa da ‘yan Najeriya cewa babban taron APC da ke tafe a 26 ga watan Maris zai zo cikin nasara duk da ɗumbin matsalolin cikin gida da su ka yiwa jam’iyyar katutu.

Naira 620 ne albashina na farko lokacin ina Malamin jami’a, cewar mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana yadda komai ya sauya a Najeriya inda ya tuna da shekarar 1981.

Ya ce a shekarar ne ya fara koyarwa a jami’ar Legas (UNILAG) inda ya ke amsar albashi N620 kamar yadda Leadership News ta ruwaito.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]

Rubuta Sharhi