22.9 C
Abuja
Friday, December 2, 2022

An gurfanar da Collins gaban kotu akan matsar mazakutar kanin sa akan wata hayaniya da ta shiga tsakanin su

LabaraiAn gurfanar da Collins gaban kotu akan matsar mazakutar kanin sa akan wata hayaniya da ta shiga tsakanin su

An gurfanar da wani mutum gaban kotun shari’a ta Milimani, bisa zarginsa da matsewa kaninsa al’aurar sa, wanda hakan ya cutar da lafiyar jikinsa, LIB ta ruwaito.

An gano yadda mutumin mai suna Collins Cheruyot, ya ci zarafin dan uwanshi Allan Sang a babban tsaunin Nairobi, bayan zarginsa da sace mishi waya da kudinsa.

collins
An gurfanar da Collins gaban kotu akan matsar mazakutar kanin sa akan wata hayaniya da ta shiga tsakanin su

Rahotun ‘yan sanda mai gabatar da kara, James Gachoka, wanda ya karanta a kotun ya bayyana yadda Sang ya kai kara ofishin ‘yan sandan, cewa yayan shi, Colins da farko ya satar mishi wayar da takai darajar Ksh9,399 da katin dan kasarshi.

An gano yadda Collins ya kara da amfani da wayar wajen cin bashin Mshwari na Ksh12,316.

Sai dai, a lokacin da ya gano dan uwan nashi ya kai kara ofishin ‘yan sanda na Capital Hill, sai ya ci zarafin sa ta hanyar matse mishi yayan maraina, gami da kizon sa a yatsa

Babban alkalin kotun majistan, Bernard Ochoi, ya tilasta dage yankewa wanda ake zargin hukunci, bayan ya fadi ciwo a kotun, inda aka kaishi asibiti don neman lafiyar sa.

Za’a cigaba da sauran karar a ranar 24 ga watan Maris, 2023.

Gwada mazakuta ta nayi in gani ko tana aiki, Mai lalata yara maza ga kotu

Wani dan kasuwa a jihar Adamawa, Abubakar Barkindo, ya shiga hannun jami’an tsaro bayan an zarge shi da lalata yara maza biyu.

Daya daga cikin yaran shekararsa tara dayan kuma takwas kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

An samu bayanai akan yadda Barkindo, ya amsa laifin da ake zargin sa da aikatawa na lalata bayan ya ce ya gwada ne don ya tabbatar al’aurarsa tana aiki.
An zarge shi da yaudarar yaran guda biyu inda suke zuwa gidan shi da ke rukunnan gidaje 50 na Jamhutu da amfani da al’aurarsa a bakin yaran da karfi.

Yayin da mahaifin yaran yake neman su ya ga yadda maniyyi ya ke zuba daga bakunan yaran guda biyu.

Kamar yadda yace:

“Na fita ne don neman yara na a kofar gida, sai aka shaida min cewa, Barkindo ya wuce da su gidan shi. Ban ji dadin hakan ba har sai da na furta hakan a gaban jama’a. Daga nan na duba sai naga maniyyi a bakunan yara na.”

Bayan gurfanar da mutumin da ake zargin a babbar kotun majistare ta daya a ranar Alhamis 17 ga watan Fabrairun 2022, ya amsa laifin sa, wanda ya saba wa sashi na 263 a dokar shari’ar jihar.

Yayin da ya fadi dalilin sa na yin lalata da yaran ta baki, cewa ya aikata hakan ne don ya fahimci ko mazakutar sa tana aiki. Ya ce ya fuskanci matsalar rashin mikewar al’aura.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe