24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Sojoji sun yi harbi a kasuwa wanda ya yi ajalin ‘yan mata guda biyu a Jihar Kaduna

LabaraiSojoji sun yi harbi a kasuwa wanda ya yi ajalin 'yan mata guda biyu a Jihar Kaduna

Wasu ‘yan mata guda biyu sun rasa rayukansu sanadiyyar harsasan da sojoji suka harba a kasuwan gundumar Kidandan, wata anguwa karkashin karamar hukumar Giwa dake jihar Kaduna, LIB ta ruwaito.

Kamar yadda ganau suka bayyana, sojojin sun tuko motarsu ta cikin kasuwa, yayin da suka hango wasu mutane zaune akan barubura, hakan yasa suka fara yi musu tambayoyi.

Sojoji sun yi harbi a kasuwa wanda ya yi ajalin 'yan mata guda biyu a Jihar Kaduna
Sojoji sun yi harbi a kasuwa wanda ya yi ajalin ‘yan mata guda biyu a Jihar Kaduna

Mazauna kauyen sun ranta a na kare, a lokacin da suka fara jin karar harbin bindigar da ake zargin sojojin ne suka bude wa wadannan mutanen wuta.

Yayin luguden wutar, ‘yan mata guda biyu, Nuratu, mai shekaru 16 da Khadija, mai shekaru 11, sun samu harbin harsasan a lokacin da suka yi kokarin tserewa daga wurin.

Babban yayan su, Salisu Shuaibu Kidandan, ya bayyana wa Daily Trust yadda yaran suka rasa rayukansu sanadiyyar harsasan da sojojin suka harba a cikin jama’a.

“Duk da sun yi ( sojojin) nufin harbin Fulanin da suka gani a kasuwar, don me zai sa su harba cikin taron mutane?

“Yan uwa na sun yi kokarin tserewa zuwa gida, saboda kasuwa na wajen garin kauyen, yayin da aka bude musu wuta,” a cewarsa.

A halin yanzu da muke magana, sojojin basu zo yi wa iyayenmu ta’aziyya akan abunda suka aikata ba, ‘yan sanda ne kadai suka yi hakan.

“Muna bukatar a yi mana adalci, saboda baza a halaka salahan yara haka kawai a tafi ba,” a cewarsa.

Haka zalika, wani mazaunin kauyen ya ce, bai kamata ace sojojin sun yi harbin a kasuwa ba, saboda Fulanin sun yi nufin tserewa cikin daji ne.

Sojojin Najeriya sun fatattaki ‘yan ta’addan ISWAP, sun kwato awaki 500

Dakarun sojojin Najeriya na Operation Hadin Kai a jihar Borno sun yi nasarar ƙwato awaki 500 a hannun ‘yan ta’addan ƙungiyar Islamic State West Africa Province (ISWAP) a ƙaramar hukumar Jere ta jihar Borno.

Jaridar Daily Trust ta samu cewa anyi ‘yar gajeruwar musayar wuta tsakanin sojojin da ‘yan ta’addan na ISWAP, wacce ta yi sanadiyyar mutuwar wasu daga cikin mambobin ‘yan ta’addan.

Wata majiya ta bayyana cewa makiyayan sun turo saƙon neman agajin gaggawa ga kwamandan rundunar atisayen Lafiya Dole, Major General Chris Musa, inda su ka sanar da shi satar awakin da aka tafka musu.

Sojojin sun bi bayan ɓarayin awakin inda su ka ritsa su a kusa da wata gonar cashew. Sun yi musayar wuta da su wacce ta yi sanadiyyar mutuwar biyar daga cikin su, yayin da sauran su ka ranta ana kare su ka bar awakin. Majiyar sojin ta tabbatar

Dakarun Najeriya sun samu nasarar kashe mayakan ISWAP 16 a jihar Borno

A ranar Litinin ne dakarun rundunar sojin Najeriya suka samu nasarar kashe akalla ‘yan ta’addar ISWAP guda 16 a karamar hukumar Jere dake jihar Borno.

Jaridar PR Nigeria ta ruwaito cewa dakarun sun kashe ‘yan ta’addar a kokarin da suke na dakile harin ta’addanci da suka kai kauyen Chabbal a wannan yanki.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe