22.9 C
Abuja
Friday, December 2, 2022

An cafke wata mata da ta yi fasa kwaurin hodar Inblis mai nauyin kilo daya da rabi 1.5kg zata shiga da ita cikin garin Madina

LabaraiAn cafke wata mata da ta yi fasa kwaurin hodar Inblis mai nauyin kilo daya da rabi 1.5kg zata shiga da ita cikin garin Madina

Hukumar kasar Saudiyya ta cafke wata mata da tayi fasa kwaurin hodar Iblis ta shiga da ita har cikin garin Madina.

Abin da yake bako shine , mai fasa-kwaurin mace ce, kuma ta sanya hodar a cikin takalmi, inda ta sanya wata kuma a cikin jakarta ta hannu hankalinta kwance.

hodar iblis
An cafke wata mata da ta yi fasa kwaurin hodar Inblis mai nauyin kilo daya da rabi 1.5kg ta shiga da ita cikin garin Madina

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasar saudiyya , sun kama matar ne a ranar Talata , kuma suka yada bidiyon da suka dauka akan lamarin , a yanar gizo.

Mutane da yawa sun girgiza ,inda wasu suka dinga tofin allatsine , wasu kuma sun kasa cewa uffan.

A gefe guda kuma, mutane da yawa sun yabawa mahukuntan jami’an kasar Saudiyyar Saboda kokarin da sukeyi wajen danke duk masu laifuka irin wadannan. 


Wani mai amfani da tweeter yayi sharhi, inda yake cewa, “Na jinjina muku sosai “. 


Wasu kuma cewa suke yi, basu yarda wai macece tayi safarar hodar Iblis din ba. Wasu kuma cewa sukeyi, ayi bincike sosai, domin matar mai yiwuwa daga wata babbar kungiyar yan safarar miyagun kwayoyi ce. 


Wannan ba shine lokaci na farko da ake kama irin wadannan laifuka ba. Akwai laifuka da dama da suka shafi safarar miyagun kwayoyi da hukumar Saudiyyar suka kama.

Kama laifin safarar hodar ba shine na farko ba

Mutane sun sha kokarin shiga da kwayoyi cikin kasar ta mabanbanta hanyoyi. Wasu ma suna daukar kwayoyi masu yawa da tunanin zasu iya ketarewa dasu. 


A watan Maris  na shekarar 2021 kadai, yan sandan iyakar kasar, sunyi nasarar cafke mutane 7 da suka yi yunkurin shiga da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 618 cikin kasar. 


A Wannan shekarar kuma, an kama wadansu yan fasa kwaurin da suka so shiga da kwayoyin Captagon masu nauyin giram dubu goma sha bakwai 17,000 cikin kasar Saudiyyar. 


Rahoton hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Saudi Arabia 


A Wannan shekarar, a filin jirgin sama na kasa da  kasa na ‘King Abdulaziz, an kama fasinjoji da yawa masu dauke da miyagun kwayoyi a tare dasu. 


Kuma dai a wannan shekarar fasinjoji da dama sunyi kokarin yin fasa kwaurin hodar Iblis mai nauyin giram 925.8 da kuma kwayoyin tramadol 4,972 da aka hana shiga dasu cikin kasar ta Saudiyya.

Zargin safarar hodar Iblis: Yadda Abba Kyari ya yi aiki da ƙungiyar ƙwaya a Brazil – NDLEA

Hukumar ‘yan sanda ta ba da sanarwar damƙe Abba Kyari a ranar litinin da ta gabata ne dai bayan kiran da aka yi na nemansa ido rufe game da safarar miyagun kwayoyi kamara yadda NDLEA ke zarginsa.

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa, NDLEA, ta nesanta jami’anta daga cinikin hodar ibilis mai nauyin kilogiram 25 da suka haɗa kai da gungun ‘yan sanda ƙarƙashin jagorancin mataimakin kwamishinan ‘yan sanda da aka dakatar, Abba Kyari.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe