Hukumar kwastan ta yi babban kamu ta cafke shinkafa da man fetur na kimanin miliyan 587

  • Post author:
  • Reading time:5 mins read
You are currently viewing Hukumar kwastan ta yi babban kamu ta cafke shinkafa da man fetur na kimanin miliyan 587

Hukumar kwastan ta shiyyar A a jihar Legas ta kwace kayayyaki da dama a hannun ma su fasa kwauri waɗanda su ka haɗa da shinkafa, man fetur, naman kaji da sauran su a watan Fabrairun 2022. Jaridar Punch ta rahoto

Anyi ƙarin haske dangane da lamarin

Kwantirola mai riƙon kwarya na shiyyar A, Hussein Ejibunu, wanda ya tabbatar da lamarin ya bayyana cewa darajar kuɗin kayayyakin ta kai N587,901,165.

Hukumar kwastan
Hukumar kwastan ta yi babban kamu ta cafke shinkafa da man fetur an kimanin miliyan 587

Ya bayyana cewa:

Wannan shine karo na biyu a cikin wannan shekarar da mu ke ganawa da ‘yan jarida. Kamar yadda aka saba maƙasudin zaman shine bayyana ayyukan hukumar na watan Fabrairu. Duk da komawa bayan da aka samu wajen harkokin kasuwanci, jajircewar jami’an mu ta sanya mun samu nasarori da dama a cikin wannan lokacin

Kayayyakin da aka ƙwace a tsakanin 3 zuwa 28 ga watan Fabrairun 2022, sun haɗa da buhuna 6,749 ma shinkafa wacce ta ke daidai da nauyin tirela, litar man fetur 36,575; dila 599 na gwanjo; kwali 906 na naman kaza; tayoyi 2,00; kwali 180 na sabulun ƙasar waje.

Firij na hannu guda 52; kwali 285 na magunguna; ababen hawa guda 13; kwali 338 na maganin sauro. Dukkanin su na da kuɗin harajin da su ka kai N587,901,165. Kuɗin da aka samu daga sayar da man fetur ɗin sun kai N79,067,560.75

Fasa ƙwauri yayi ƙamari a yankin kudu maso yamma

Ejibunu ya bayyana cewa yankin kudu maso yamma ya zama waje mai wahalar gudanar da ayyuka ga masu fasa ƙwauri a cikin yan kwanakinnan, inda ya ƙara da cewa kowa nada rawar da zai taka wajen daƙile fasa ƙwauri.

Ya ƙara da cewa:

Kamar yadda na sha faɗa a baya, sai an haɗa hannu da karfe. Hana fasa ƙwaƴri yana buƙatar haɗin kan kowa da kowa. Dole ne mu yaƙi fasa ƙwauri saboda illolin sa ma su tarin yawa.

Hukumar Kwastan ta kama naman Jaki a buhunhuna har guda 1, 390 yayin da ake kokarin safarar su

Hukumar kwastan ta Najeriya ta yi nasarar ganowa tare da cafke wasu buhunhuna dake makare da naman Jaki ha guda 1, 390, a kokarin da ake yi na safarar su da jahar Kebbi, zuwa wani bangare na kasar Nageriya da ba’a bayyana ba. 


Jami’in hukumar kwastan mai kula da shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya dake jihar ta Kebbi, Joseph Attah, ya bayyana kimar kudin naman Jakin da suka kama, inda yace zasu kai kimanin Naira miliyan arba’in da biyu 42, 000,000.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]

Rubuta Sharhi