Wani mai garkuwa da mutane da ya shiga hannun hukuma ya bayyana yadda ya tona asirin abokan harƙallar sa bayan sun biya shi naira dubu ɗari biyu (N200,000) kacal daga cikin naira miliyan 12 da su ka amsa a matsayin kuɗin fansar wasu mutum biyu.
Mutumin mai suna Sadu Bunkawu, wanda bai gamsu da kason da aka bashi ba, ya garzaya zuwa ofishin ‘yan sanda inda ya bayyana laifukan sa. Pulse.ng ta rahoto

Ya bayyana yadda lamarin ya auku
Bunkawu mai shekaru 28, ɗan asalin ƙauyen Filingo ne a ƙaramar hukumar Jada ta jihar Adamawa. Ya bayyana cewa an biya abokan harƙallar sa naira miliyan 12 na kuɗun fansar wasu mutum biyu Umaru Diffawa da Umaru Babidi mazauna ƙauyen.
Rashin gamsuwa da yadda aka kasafta kuɗin, ya sanya ya garzaya zuwa wajen ‘yan sanda domin su kwato masa hakkin sa.
Bunkawu ya ciza yatsa kan rashin sa’ar sa a cikin aikin inda dubu ɗari biyun da ya ƙarba ta faɗi akan hanyar sa komawa gida.
Na rasa kason da na samu a kuɗin yayin da na ke saurin komawa gida akan lokaci
Mu bakwai iyalan waɗanda aka ɗauke ɗin su ka ba kuɗin. Bayan mun sake su an kirani inda aka bani N200,000 kacal
A cewar sa
An maka shi gaban kotu
Sai dai ‘yan sanda sun maka shi gaban kotun majistare ta ɗaya a Yola bisa laifin ƙitsa laifi da yin garkuwa da mutane.
Bunkawu ya amsa dukkanin tuhumomin da ake masa inda alƙalin kotun Muhammad Abdullahi ya ɗaga shari’ar zuwa 4 ga watan Afrilun 2022.
Ku dauki makamai domin kare kanku daga ‘yan bindiga, jami’an tsaro sun gaza -gwamna ga ‘yan jihar sa
Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya buƙaci mazaunan jihar sa musamman waɗanda ke zama a ƙauyuka da su ɗauki halastattun makamai domin kare kawu nan su daga ‘yan ta’adda.
Ya bayyana cewa hakan ya zama wajibi ne saboda yanzu an wuce da yayin cigaba da kiran neman ɗauki. Jaridar Daily Trust ta rahoto
Dole ne mu kasance cikin shirin ko ta kwana wajen tunkarar ‘yan ta’adda. Wannan wata hanya ce da zamu iya taimakawa jami’an tsaro wajen daƙile wannan matsalar tunda abubuwa sun yi musu yawa.
A cewar sa
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com
Allah Mai iko yau a jahar kaduna muntashi da hazo sosai hartakai bama ganin junan mu daga nesa Allah mungodema