27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Sabon Salo: yadda aka raba Garin kwaki da kankara a wani taron biki ya ja hankalin Mutane

LabaraiSabon Salo: yadda aka raba Garin kwaki da kankara a wani taron biki ya ja hankalin Mutane
8d6a997b5c6be4ea
yadda aka raba garin kwaki a wani bikin aure

Shinkafa ita aka sani a gidan biki ba garri ba

Abu ne da ya zama kamar Doka a Najeriya idan za ayi Biki shinkafa ita ce abinci da ake ciyar da baki; Amma abin mamaki an ga wani faifan bidiyo na wani taron biki da aka raba garri. Wani mai yada abubuwa a shafukan sada zumunta, Tunde Ednut ya wallafa wani bidiyo a shafin Instagram na wani taron biki da aka yi mai lakabi da bikin garri,ta re da mamakin yadda al’amura ke saurin canzawa a kasa Najeriya.

Manyan baki sun chaba ado suna lomar Gari

A cikin faifan bidiyo, an hangi manyan baƙi sun chaba ado da kwalliya kowannen su yana dauke da tiren katako shake da garri, abincin teku, ice krem da ruwan kwalba.
Duban garri ɗaya daga cikin baƙin, wanda da alama hankalin ta baya jikinta tsabar dadi,hadda kankara a ciki.
Da alama dai bakin suna da masaniyar irin abincin da za a raba musu, lura da cewa kowannen su yana cin abinci hankali kwance batare da wani chanza fuska ba.

Mutane da da dama sun yaba wa wannan sabon tsari

@bettyjb_ ya ce: “hakan yayi kyau. Na tuna da kanwar mahaifiyata (Allah ya jikanta) ta saka yankan kosai ƙananan yanka ta kawo wajen bikin aure na, ban sani ba har sai da wani ya zo ya tambaye ni ‘yaya ?, wa ke rike da kosai’,na ce akara kuma? . Da na tambaye ta sai ta ce ta siya ne, ba tare da ta na ds tabbacinko mutane za su so shi ba.

@devdammak ya ce: “@oseun01 irin wannan abincin za a raba ranar bikin aurenmu ooooo… mu je kawai mu je Ijebu smu sayi buhunan Garri 2, mu sayi cartoon 3 na Eja panla, a sayo kanakara da Sikari… watakila a dan kara da mangyada … Bikin aure ya kayatar.”

@trjfootwear ya ce: “Na tuna lokacin muna kanana a lokacin idan muna son zagi sai mu ce, ku je ku sha garri ranar oo ga shi kuwa ya tabbata.”

@adeodi1 ya ce: “Wannan abu ne mai ban mamaki! Idan za mu iya cin abinci kasar chana, abinci Mexika ko wasu a matsayin abincin alatu, ya kamata kar mu nuna girman kai ga na mu abincin. Omo eni o le se idi bebe ka tun maa wo ileke si idi omo elomi!”

Gurguwar budurwa mai shekaru 70 ta ce saurayi danye shakaf mai shekaru 21 take so ta aura

Wata budurwa ‘yar shekara 70, mai suna Genevieve, wacce bata taba kusantar wani ba, duk ba ita ta zabi hakan ba; sai dai a cewarta haka rayuwa tayi da ita, Legit.ng ta ruwaito.
Genevieve tana fama da matsalar gurgunta, hakan ya tilasta mata rarrafe saboda bazata iya amfani da kafar ta ba; bata taba tafiya ba a rayuwarta.
Kuma bata taba saurayi ba ko samun ilimi ingantacce.
Yayin zantawa da Afrimax, gurguwar budurwa ta ce, an haifeta a shekarar 1952.
Sai dai, a lokacin da iyayen ta suka farga diyar tasu bata iya tafiya, cigaba da rarrafe tayi. Sun yi zaton lamarin zai canza idan ta kara tasawa, amma hakan bai kasance ba.

Budurwar ta bayyana yadda tayi fama da cuta a lokacin da tana yarinya, wanda hakan ne ya shafi kafarta, kuma yasa ta zama lalura ga iyayenta.
Iyayen Genevieve basu tura ta makaranta ba, saboda basu da kudin siya ma ta kujerar guragu, sannan ba za su iya kai ta da dawo da ita kullum ba.

Baya ga rashin samun damar neman ilimi, halin da take ciki ya hana ta samun masoyi

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe