Watanni Biyu Da aka yi masa dashen zuciyar Alade, David Benett ya Mutu

  • Post author:
  • Reading time:5 mins read
You are currently viewing Watanni Biyu Da aka yi masa dashen zuciyar Alade, David Benett ya Mutu
531b7168da954dd3
Benett David da akayi ma dashen zuciyar ALade

An dasa masa zuciyar Alade don cigaba da rayuwa

Watanni biyu bayan da duniya ta yi bikin murnar nasarar dashen zuciyar Alade da aka yi wa David Benett, ya kwanta dama. Likitoci a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Jami’ar Maryland sun bayyana hakan a ranar Laraba, 9 ga watan Fabrairu, shekarar 2022, cewa Bennett mai kimanin shekaru 57 ya mutu kwana daya bayan da jikinsa ya fara tsananta.

Abin da likitocin suka ce game da mutuwar Bennett

Wata sanarwa da ta fito daga Cibiyar Kiwon Lafiya ta Maryland ta ce lokacin da aka fahimci cewa David Bennett ba zai warke ba, sai aka ba shi kulawar jinya na musamman don ya samu damar ganawa da iyalinsa a cikin sa’o’insa na ƙarshe.

Ko mutuwar sa na da alaka da dashen zuciyar da akayi masa?


Har yanzu ba a gano musabbabin mutuwarsa ba kuma ba a sani ba ko mutuwar sa tana da alaka da dashen zuciyar da aka yi masa. Dan sa ya mika godiyar sa ga likitoci bisa kokarin su a kan abin da suka aikata. A wani bayani da asibitin ya fitar, Dansa ya jinjina wa asibitin a bisa ƙoƙarinsu da kuzarinsu, wajen ganin mahaifin su ya rayu, tare da irin kwarin gwiwar da suka basu lokacin jinyar shi.

Ya kudiri Aniyar ci gaba da rayuwa

Ɗansa, David Bennett Jr. ya ce har zuwa lokacin mutuwarsa, mahaifinsa ya kuduri aniyar kokarin ganin ya warke domin ya yi rayuwa cikin iyalansa da kuma dangin sa, wanda suka hada da ‘yan uwansa mata biyu, ‘ya’yansa biyu, jikoki biyar da karensa, Lucky. Matashi Bennett ya ce sun sami damar ganawa da mahaifinsu na tsawon makonni yayin da ya murmure daga tiyatar da aka yi.


Wani Likita a kasar Saudiyya ya gana da wasu tagwaye da ya raba shekaru 13 da suka gabata

‘Yan biyun lokacin da aka haife su an haife su ne a manne da juna a kasar Saudiyya. Yawancin gabobin jikinsu kamar su hanji da mafitsara suna hade ne wuri daya.
Abdallah Al-Rabiah, babban mai kula da Cibiyar Bayar da Agajin Gaggawa ta Sarki Salman (KSrelief), ya gana da Hassan da Mahmoud a ranar Laraba wadanda a da sassan jikin su yake a hade. ‘Yan asalin kasar Masar ne, amma mazauna birnin Riyadh, kimanin shekaru 13 kenan bayan da aka yi nasarar raba su a wani aikin tiyata da aka yi musu a garin Riyadh.
Likitoci a asibitin King Abdulaziz Medical City sun yi wa tagwayen tiyata a shekarar 2009 a lokacin da suke da watanni 9 kacal. An hade su a cikin ciki kuma an raba wasu gabobin jiki da sassan jiki, ciki har da hanji da kuma fitsari.

Al-Rabiah ya ce masarautar za ta ci gaba da zama fitila ga mabukata da marasa galihu a duk fadin duniya. Shirin likitancin da aka raba Hassan da Mahmoud, wani karin girma ne na ayyukan jin kai na kasar, in ji wanda ake gudanarwa a karkashin umarnin Sarki Salman da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman na kasar Saudiyya.
Tagwayen dai sun samu rakiyar iyayensu ne a ziyarar da suka kai babban birnin kasar Saudiyya, inda suka gode wa jama’a da gwamnatin kasar Saudiyya bisa shirya yi wa ‘ya’yansu tiyata. Lafiyar yaran ya inganta a tsawon shekaru, in ji su.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Rubuta Sharhi