Hukumar Kwastan ta kama naman Jaki a buhunhuna har guda 1, 390 yayin da ake kokarin safarar su

You are currently viewing Hukumar Kwastan ta kama naman Jaki a buhunhuna har guda 1, 390 yayin da ake kokarin safarar su
Kwastan ta kama naman Jaki a buhunhuna har guda 1, 390 yayin da ake kokarin safarar su

Hukumar kwastan ta Nageriya ta yi nasarar ganowa tare da cafke wasu buhunhuna dake makare da naman Jaki ha guda 1, 390, a kokarin da ake yi na safarar su da jahar Kebbi, zuwa wani bangare na kasar Nageriya da ba’a bayyana ba. 


Jami’in hukumar kwastan mai kula da shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya dake jihar ta Kebbi, Joseph Attah, ya bayyana kimar kudin naman Jakin da suka kama, inda yace zasu kai kimanin Naira miliyan arba’in da biyu 42, 000,000.

Ya kara da cewa :

” Daya daga cikin dillalan safarar naman Jakin ya fada mini cewa, sai da suka gintile Jakai har guda dubu daya kafin su iya tara wannan dimbin naman “. 


Kwantirolan ya kara da cewa, a kwai haramcin doka ga safarar nau’in naman dabbobin da ba’a yarda a ci naman su ba. Inda ya kawo sadara a cikin sashe na 63 karamin sashe na ba a cikin baka (b) wadda ta haramta hakan daga cikin kundin tsarin dokokin hukumar ta kwastan.

donkey
Kwastan ta kama naman Jaki a buhunhuna har guda 1, 390 yayin da ake kokarin safarar su

Yan sanda sun ceto waɗanda ake yunkurin safarar su, sun dakile harin ‘yan bindiga a Katsina

‘Yan sanda sun ce an ceto mutanen da aka yi yunkurin safararsu daga yankin kudancin Najeriya a wani gari mai iyaka da Jamhuriyar Nijar.

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce ta ceto mutane bakwai da aka yi garkuwa da su tare da dakile wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai kauyen Fadimawa da ke karamar hukumar Kurfi a jihar.

Da yake zantawa da manema labarai da yammacin ranar Juma’a, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, Gambo Isa, ya ce an kuɓutar da wadanda aka yi safararsu daga yankin kudancin ƙasar ne a kauyen Koza da ke ƙaramar hukumar Mai’adua, mai iyaka da Jamhuriyar Nijar.

“A yayin gudanar da bincike, wadanda lamarin ya rutsa da su sun bayyana cewa, wakilin su ne ya kawo su kauyen, inda suka ga tawagar ‘yan sandan, sai suka gudu da wayoyin su na GSM.

“Sannan kuma sun bayyana cewa suna kan hanyar su ne daga Najeriya zuwa Libiya ta kan iyakar Jamhuriyar Nijar. Ana ci gaba da bincike, za a mika su ofishin NAPTIP da ke Kano, domin ci gaba da bincike tare da damƙe ɓarayin,” yace.

Wadanda aka ceto sun hada da: Success Oshoopkeme, Isaac Debora, Amoruwa Ade, James Rebecca, Emmanuel Godwin, Zainab Tijjani, da Taofik Olawale.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]

Rubuta Sharhi