Jerin mata 8 ‘yan Najeriya da suka yi ‘na farko’ a fannoni daban-daban

  • Post author:
  • Reading time:8 mins read
You are currently viewing Jerin mata 8 ‘yan Najeriya da suka yi ‘na farko’ a fannoni daban-daban
Jerin mata 8 'yan Najeriya da suka yi 'na farko' a fannoni daban-daban

Domin Ranar Mata ta Duniya, muna bikin mutane takwas na gaba-gaba a fannoni daban-daban, Pulse.ng ta jero sunayen su da kuma rawar da suka taka.

Matan Nijeriya sun kasance a sahun gaba a tarihi, kasancewarsu mayaƙa marasa tsoro irin su Sarauniya Amina, mata masu sadaukarwa irin su Moremi da masu fafutuka irin su Funmilayo Ransome-Kuti da Alimotu Pelewura.

  1. Ngozi Okonjo-Iweala
ngozi
Ngozi Okonjo-Iweala

Ngozi Okonjo-Iweala, ita ce mace ta farko da aka naɗa a matsayin shugabar ƙungiyar ciniki ta duniya, WTO. Ta kasance a wani ɓangare na Times Magazine 100 masu tasiri a duniya.

  1. Elizabeth Awoliyi
elizbth
Elizabeth Awoliyi

Elizabeth Awoliyi ita ce Likita mace ta farko a Najeriya.

  1. Virginia Etiaba
virginia
Virginia Etiaba

Virginia Etiaba ita ce mace ta farko da ta yi gwamna a tarihin Najeriya. Ta zama gwamna ne a shekarar 2006 bayan an tsige Peter Obi, amma sai da aka dawo da shi cikin watanni uku don haka sai ta sauka daga mulkin.

  1. Chinyere Kalu
chinyere
Chinyere Kalu

Chinyere Kalu ita ce mace ta farko a Najeriya matuƙiyar jirgi na kasuwanci kuma mace ta farko da ta fara tuka jirgin sama a Najeriya.

  1. Folake Solanke
folake
Folake Solanke

Folake Solanke ita ce Lauya ta farko da aka bai wa mukamin ta babbar lauya a Najeriya.

  1. Aloma Mariam Mukhtar
aloma
Aloma Mariam Mukhtar

Ita ce lauya mace ta farko daga Arewacin Najeriya, mace ta farko mai shari’a a babbar kotun jihar Kano, kuma mace ta farko mai shari’a a kotun ɗaukaka ƙara ta Najeriya sannan kuma mace ta farko a kotun ƙolin Najeriya.

  1. Tolulope Arotile
tolutope
Tolulope Arotile

Tolulope Arotile, ita ce mace ta farko da ta zama mai tuka jirgi mai saukar ungulu na yaƙi a rundunar sojojin saman Najeriya. Ta mutu a wani hatsarin mota a watan Yuni 2020.

  1. Funmilayo Ransome-Kuti
funmilayo
Funmilayo Ransome-Kuti

Ita ce mace ta farko da ta hau mota a Abeokuta. Ta kasance ‘yar gwagwarmayar siyasa kuma mahaifiyar fitaccen mawaki kuma ɗan gwagwarmaya Fela Anikulapo Kuti.

Jerin jaruman Kannywood mata 4 masu hawa motoci masu tsadar gaske

A lokuta da dama mutane na yawan sanya alamar tambaya kan yadda wasu daga cikin jaruman mata ke tafiyar da rayuwar su, musamman ma yadda suke kashe makudan kudade wajen sayen kayan kyale-kyale na rayuwa.

Hakan ya sanya wasu ke yawan tambayar a ina suke samun irin wadannan kudade da suke irin wannan rayuwa da su, tabbas kowa ya san da yawa daga cikin jaruman banda sana’ar da suka saba ta Kannywood suna hadawa da kasuwanci da kuma ‘yan sauran abubuwan da ba a rasa ba.

A wannan karon Labarun Hausa ta binciko muku jerin manyan jaruman Kannywood mata da suke hawa dankara-dankaran motoci na kece raini:

1. Jaruma Hafsat Idris

Ta siya motar kirar Formatic, mai tsadar kimanin Naira miliyan goma sha bakwai (N17,000,000).
A lokacin da ta siya ta girgiza masana’antar Kannywood kwarai. Ta kuma wallafa hotunan motar a shafinta na Instagram inda ‘yan uwa da abokai su ka dinga yi mata fatan alkhairi.

Abokan sana’arta ma sun dinga wallafawa a shafukansu su na mata fatan alkhairi ciki har da sarki Ali Nuhu wanda ake yi wa kallon aboki kuma amininta a masana’antar

2. Jaruma Hadiza Gabon

Motar Hadiza ta kamfanin Honda wacce aminiyarta a lokacin, Laila Ali Usman ta bata.

A lokacin jarumar ta wallafa a shafinta na Instagram inda ta nuna godiyarta kwarai ga kawar. Farashin motar ya kai naira miliyan goma sha daya(N11,000,000).

3. Motar Jamila Nagudu

Shahararren mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya ba jarumar kyautar mota kirar Toyota Matrix.

A shafin Rarara Multimedia na instagram mawakin ya wallafa bidiyo inda aka ga ya na ba jarumar kyautar motar inda ta nuna farincikinta kwarai.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]

Rubuta Sharhi