23 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Yadda aka yi min korar kare daga gidan haya kafin Allah ya azurta ni, Rukayya Dawayya

LabaraiKannywoodYadda aka yi min korar kare daga gidan haya kafin Allah ya azurta ni, Rukayya Dawayya

Tsohuwar jarumar Kannywood kuma ‘yar kasuwa, Rukayya Umar Dawayya ta bayar da labarin yadda wani mutum ya kore ta daga gidan haya a lokacin da bata da gidan kan ta,.

Kamar yadda ta wallafa bidiyo tana bayar da labarin wanda Tashar Tsakar Gida ta YouTube ta wallafa, ta ce a lokacin tana farkon shiga Kannywood iyayenta suka nuna ba sa son ta yi fim.

rukayya d
Yadda aka yi min korar kare daga gidan haya kafin Allah ya azurta ni, Rukayya Dawayya

Ta ce kawarta ce ta zuga ta wacce take fim inda ta bijire wa iyayenta ta bukaci su hada kudi don su kama gida wanda ta amince.

Ta shaida yadda suka samu gida tare da gayyatar ‘yar uwar mahaifiyar wannan kawar ta wacce take zama da su a gidan.

Bayan bai wuce kwana 3 da kama gidan ba yara suka fara cika a kofar gidan suna kiran ta ko ta ina, kasancewar ta yi fim an san ta, daga nan mai gidan ya lura ya fusata da yadda mutane suke zuwa gidan.

Ta ci gaba da bayyana yadda aka shaida wa mutumin cewa su ‘yan fim ne, hakan yasa da asuban fari ya je ya watso musu kayan su a waje ya wulakanta su.

Kamar yadda ta ce:

“A takaice ba a fi shekara 3 ba Allah ya kawo fatahi, kun san shi arziki nufin Allah ne. Kuma Allah yana ba wanda yane so da wanda baya so arziki. Saboda haka mutum karimi mutumin kirki shi ne wanda Allah ke so amma Allah yana ba wanda yake so da wanda baya so arziki.

“Ba a je da nisa ba bayan al’amura sun kankama na samu dan jari na da sauran su. Sai wani bawan Allah ya bukaci in siya gidansa a nan Kano a Unguwa Uku, yana cikin matsala.”

Ta bayyana yadda ta siya gidan kuma ta ba ‘yan hayar gidan notis akan su tashi don tana so ta yi gyara.

Wata rana ta dawo daga Umra sai aka ce mata wani mutum yana ta zuwa neman ta ba ya samun ta. Cewa yana neman alfarma ba ya da kudin da zai kama wani gida tunda ta bayar da notis ga shi da yara har da matarsa.

Da ta bukaci a yi musu iso sai ta gano cewa shi ne wannan mutumin da ya yi musu wulakanci a baya har ya kore su daga gidansa da suka yi haya.

Ta bayyana mamakin ta inda ya dinga bata hakuri tare da neman ta taimaka masa. Ta amince ya ci gaba da zama a gidan har ranar da Allah zai ba shi nashi gidan.

A cewarta, har yanzu yana nan zaune a gidan nata ba tare da yana biyan sisin kwabo ba duk da wulakancin da ya yi mata a baya.

Duk namijin da ya ke barin matarsa ta na rawar TikTok ba zai ji kamshin Aljannah ba, Jaruma Rukayya Dawayya

Jaruma Rukayya Dawayya a wani bidiyo da ta yi wanda Hadiza Gabon ta wallafa a shafinta na Facebook ta ja hankali ga mata musamman masu aure da su ke raye-raye a shafukansu na TikTok.


Jarumar ta fara ne da bayar da wani labari takaitacce wanda ta ce ya auku da ita a lokacin tana da aure.


Jarumar ta fara da bayyana yadda wasu shakikan kawayenta su ka kai mata ziyara gidanta da ke Abuja bayan ta ci kwalliya amma mijinta bai gani ba.

Tun samun labarin sun kai mata ziyarar our ta nuna a sanar dasu cewa bata nan duk don kada su ga kwalliyarta kafin mijinta.
A cewar jarumar, har sai da mijinta ya dawo ya ga kwalliyar sannan daga bisani ta kira su ta ce musu ta dawo daga inda ta je.


Daga karshen bidiyon ta ce duk macen da ke yin kwalliya ta wallafa bidiyon kwalliyar a TikTok bata son mijinta, yayin da mazan da su ke barin matansu su na bidiyon ba sa kaunar matan kuma basa kishinsu.
Jarumar ta ce ko kamshin Aljannah namiji mara kishi ba zai ji ba, saboda hakan fadin manzon Allah (SAW) ne.
Ta ce da ace mata za su ga wasu mazan da ke kallon bidiyonsu na TikTok da ba su yi ba tun farko da har kuka sai sun yi.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe