29 C
Abuja
Saturday, December 3, 2022

Bayan watanni 7, auren sirrin da Zarah Diamond ta yi ya mutu

LabaraiKannywoodBayan watanni 7, auren sirrin da Zarah Diamond ta yi ya mutu

Tashar Tsakar Gida ta bayyana yadda suka samu labari akan mutuwar auren da Zara Diamond ta yi a sirri a watanni 6 zuwa 7 da suka gabata.

Kenan ta bi sahun su Rahama Hassan, Hafsat Shehu da su Mansura Isah.

diamond z
Bayan watanni 7, auren sirrin da Zarah Diamond ta yi ya mutu

Tsawon lokaci kenan da Zara Diamond ta bude shafukan sada zumunta na Instagram da TikTok inda take wallafe-wallafen ta cike da nishadi.

A kwanakin nan ne abubuwa suka sauya salo don a lokacin da ta yi auren sirri ta goge duk wasu shafukanta na kafafen sada zumunta kuma ta bukaci shafukan masoyanta wato Fan Page da su goge don ta yi aure.

Tun bayan auren ta, ba a fiye ganin jarumar ba sai a kwanakin nan da abubuwa suka sauya inda ake ganin tana bidiyo da kananun kaya kuma babu dankwali akanta.

Wannan sauyin yasa mutane suka fara sanya alamun tambaya domin lamarin da mamaki, don ko hoto ta daina wallafawa ballantana batun bidiyo.

Wata majiya ta tabbatar wa Tashar Tsakar Gida cewa tabbas aurenta ya dan jima da mutuwa sai dai bata riga ta bayyana bane.

Hakan yasa Tashar Tsakar Gida ta tuntubi wani furodusa da ke da alaka da ita, Sunusi Multimedia don ya bayar da lambar wayanta a ji daga bakin ta.

Sai dai ta tura sako cewa a lokacin da zata yi auren ta babu wani dan jarida da ta tuntuba, don haka bata ga dalilin da zai sa a dame tada tambayar auren ta ya mutu ko kuma bai mutu ba.

Da fatan Allah yasa hakan ne mafi alkhairi, Ameen.

Auren Rahama Hassan ya mutu, ta dawo harkar Kannywood

Wani bidiyo ya fara yawa a shafukan sada zumuntar zamani wanda fitaccen furodusa, Abubakar Bashir Maishadda ya wallafa a shafinsa ya dauki hankulan mutane da dama.

A bidiyon, wanda Tashar Tsakar Gida ta nuna, an ga tsohuwar jarumar tare da sauran jarumai sanye da hula ta kungiyar mawaka da jarumai ta 13 X 13, inda mai shaddan ya rubuta “Rahama Hassan is back” ma’ana “Rahama Hassan ta dawo”.

Wannan bidiyon ne ya kara bayar da tabbacin cewa auren Rahama Hassan ya mutu saboda babu yadda za ayi da aurenta ta dawo fim har su kai ga yin tsayuwae gab da gab da MaiShadda.

Musamman idan mutum ya kalli yadda jarumar ta dakata da yin fina-finai tun kafin ta yi aure har ta kai ga yin aure.

Bayyanar Rahama Hassan a daidai lokacin da ‘yan fim suke ta aure ya janyo surutai inda wasu suke cewa dama ko sun yi aure ba sa son zama.

Dama tun a bayan an fi bayar da misalin masu zaman aure kamar ita jaruma Rahama Hassan din, Mansura Isah, Maijidda Abdulkadir, Wasila da sauran su.

Duk da dai akwai wasu jaruman da auren su yake mutuwa amma basa dawowa fim wanda hakan yake sa asirin su ya rufu.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe