2023 : Ina yin tattaki daga Abuja zuwa Legas a kafa saboda kaunar Tunibu – Inji wani matashin Bakano

You are currently viewing 2023 : Ina yin tattaki daga Abuja zuwa Legas a kafa saboda kaunar Tunibu – Inji wani matashin Bakano


Hassan Lawan, wani dan garin Durun, dake karamar hukumar Kabo ta jihar Kano, ya fara tattaki ranar Laraba tun daga Abuja zai je Legas, domin nuna goyon bayan sa ga takarar Shugabancin kasa ta jagoran jamiyyar APC, Bola Ahmad Tunibu. 

Lawan din dan shekara 30, ya gana da yan jarida, gabanin tafiyar tasa ta bakin mashigar Abuja. 
Yana rike da wata karamar jaka da kuma hoton Tunibu wanda ka rubuta : ‘ Domin dorewa daga inda aka tsaya, Tunibu shine amsa kuma shine kyakkyawan cike gurbin Baba ‘ .


Yace :

” Ina so in yi sadaukarwa a madadin matasan Najeriya, inda zanyi tattaki tun daga Abuja har Legas domin inje na roki Asiwaju Bola Ahmad Tunibu, ya daure ya fito takara domin ya zama shugaban Najeriya bayan Buhari ya kammala. 


tunibu
Asiwaju Bola Ahmad Tunibu

” Idan dan kudine, to shi face yana da kudi. Kawai shi yana sone ya kawo kyakkyawan canji ga Nageriya. Yana bukatar karfin iko domin ya kawo kyakkyawan sauyi ga matasan Najeriya wadanda kuke ta shan wahala a hannun mahukunta da suka gabata. 

“Sabo da haka daga nan mashigar Abuja zan yi tattaki har jihar Legas, inda zan karkare tafiyar a dandalin Tafawa Balewa”.

Yan Najeriya za su samu ilimi kyauta da zarar na zama shugaban kasa – Bola Tunibu

Tsohon gwamnan jihar Legas kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tunibu, ya yi alkawarin biyan kudaden jarrabawar kammala sakandare wato WAEC ga kowane dalibi dan Najeriya idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

Tinubu ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da jaridar The Cable ta yada a ranar Laraba, 19 ga watan Janairu.

Ya ke cewa :

“Za mu biya kuɗaɗen jarrabawar ‘ya’yanku na WAEC ta yadda ba za a bar kowa a baya ba a harkar ilmi, komai talaucin sa.

“Alamar jam’iyyarmu ita ce tsintsiya. Alamar hulata kuma shine ba gudu ba ja da baya zamu kawo karshen jahilci, talauci, da sauran abubuwa.

“Muna bukatar kwanciyar hankali a kasa, muna buƙatar zaman lafiya, muna bukatar dakatar da ƴan ta’adda saboda yana da matuƙar mahimmanci, domin mata sune suka fi jikatta a tashin hankulan da ke afkuwa, zamu kawo karshen rashin zaman lafiya. Idan ba zaman lafiya da kwanciyar hankali, ba za mu iya gina kasar yadda muke so ba.”

Tunibu ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyon da ya bayyana inda ya ke jawabi ga wasu kungiyoyin mata ya bukaci da su ci gaba da zama a jam’iyyar APC domin ciyar da jam’iyyar gaba.

A baya idan ba a manta ba munji cewa Bola Ahmad Tunibu ya fito ya bayyana ra’ayinsa nason tsayawa takarar shugaban kasar Najeriya, ya fara bayyana hakan ne a wata ziyara da ya kaima shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda yake nuna cewa indai talakawa zasu ba shi damar wannan kujera to fa zasu ga sauye sauye da dama ciki hadda kawo karshen ta’addanci

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku

iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]

Rubuta Sharhi