Matashin da ya bar makaranta ya kera motoci masu amfani da wutar lantarki a Maiduguri

  • Post author:
  • Reading time:5 mins read
You are currently viewing Matashin da ya bar makaranta ya kera motoci masu amfani da wutar lantarki a Maiduguri

Wani lamari mai girman gaske yana faruwa a Maiduguri, babban birnin jihar Borno. Wani matashi ɗan shekaru 29 mai suna Mustapha Gajibo yana ƙera motoci da keke mai kafa uku masu amfani da wutar lantarki sannan yana sauya fasalin injinan motoci

Matashin ya bar jami’a

Abin mamaki shine Gajibo ya bar makaranta. Ya bar jami’ar Maiduguri a shekarar 2015 bayan yakai shekara ta uku. Ya bar makarantar ne saboda an bashi General Agriculture a maimakon Electrical Engineering wanda yake matuƙar so.

Matashi
Matashin da ya bar makaranta ya ƙera motoci masuamfani da wutar lantarku a Maiduguri

Da yake magana da Legit.ng, matashin ya bayyana cewa motocin na sa a nan ƙasar ake ƙera su. Motar za ta iya tafiyar tsawon kilomita 100 zuwa 150 kafin ta buƙaci ayi mata caji.

Ga abinda yake cewa:

Eh komai da komai ana yin sa ne anan birnin Maiduguri na jihar Borno. Ina alfahari da cewa dukkan ma’aikatan da mu ke aiki da su akan wannan shirin an samo su ne sannan aka ba su horo anan gida Najeriya.

Kayayyakin matashin na samun ƙarbuwa

Gajibo ya bayyana cewa kayayyakin sa sun samu masaya anan gida Najeriya. A cewar sa da yawa daga cikin motocin sa da keken masu ƙafa uku an fara amfani da su wajen jigilar fasinjoji.

Mun samu mutane da yawa da su ke sha’awar siyen kayayyakin mu, musamman mota da keke mai ƙafa uku amsu amfani da wutar lantarki. Ya zuwa yanzu mun sayar da keke mai ƙafa uku guda 15 da motoci 7 waɗanda tuni har sun fara samarwa da waɗanda su siya kuɗaɗen shiga.

Ba a daɗe ba Gajibo ya kai ziyara gidan gwamnatin jihar Borno inda ya gabatar da motocin sa ga gwamna Babagana Umara Zulum. Gwamnan ya yaba matuƙa.

Muhimman amfanin abin sha na zoɓo ko shayin zobo guda 7 ga lafiyar ɗan Adam

Shayin zoɓo ko kuma abin sha na zoɓo, sanannen abin sha ne a yawancin yankuna na duniya, kuma galibi ana amfani da shi don dalilai na magani.
Ana yin shayin/abin shan da furen itaciyar, mai launin ja.

Akwai nau’ikan tsiron zoɓo da yawa a duk faɗin duniya ciki har da faɗin Afirka. Mafi yawan nau’ikan da ake amfani da su a cikin abin sha na zoɓo a Najeriya da duniya baki daya, ana kiransa Roselle. Bayan Afirka, hibiscus rosa-sinensis kuma an kwatanta shi da cewa yana da yawan amfani da magani a Ayurveda ta Indiya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]

Rubuta Sharhi