Robert Pattinson shi ne namijin da ya fi ko wanne kyau kamar yadda kimiyya ta tabbatar

  • Post author:
  • Reading time:5 mins read
You are currently viewing Robert Pattinson shi ne namijin da ya fi ko wanne kyau kamar yadda kimiyya ta tabbatar
Robert Pattinson shi ne namijin da ya fi ko wanne kyau kamar yadda kimiyya ta tabbatar

Binciken kimiyya ya nuna Robert Pattinson a matsayin namijin da ya fi ko wane namiji kyau a fadin duniya kamar yadda wani likitan gyara siffar bil’adama ya binciko, Culturacollectiva.com ta ruwaito.

Kamar yadda binciken na kimiyya ya nuna, gaba daya duniya babu namiji mai kyau kamar Pattison.

robertt
Robert Pattinson shi ne namijin da ya fi ko wanne kyau kamar yadda kimiyya ta tabbatar

Jarumin fina-finan Birtaniya mai shekaru 35 ya samu kaso 92.15% bisa dari tun a siffar fuskarsa kamar yadda binciken likitan, Dakta Julian De Silva ya nuna.

Likitan ya mayar da binciken sa a bangaren Golden Ratio of Beauty Phi, wani jadawali da tsofaffin Girka suka samar.

Suna amfani da jadawalin ne don ayyukan su na kirkire-kirkire.

kamar yadda binciken ya nuna:

“Yana cikin mutane 5 na sama wadanda suke da kirar fuska da hava mai kyau. A bangaren leben sa ne bai samu maki sosai ba saboda dan karami ne leben nasa.

“Ba Pattinson ne kadai sanannen mutum da aka yi bincike akan sa ba. An yi akan Henry Cavil ya zo na biyu a binciken inda ya ke da kaso 91.64%, Bradley Cooper ya zo na uku da kaso 91.08 sai kuma George Clooney mai kaso 89.91%.”

An yi amfani da digital mapping a binciken wacce take ba kwararru damar gano wanne sanannen mutum ne ya kusa kai 100%.

Wannan salon yana taimaka wa likitoci masu gyara siffar dan’ada wurin kawo gyara a kyau na halittar dan’adam kuma sun shirya salon da zasu yi amfani da shi wurin sanya abinda suka gani a jikin wani na daban.

Mun ji dadin yadda Jadawalin ya tabbatar da cewa Robert Pattinson ba dan baiwa kadai bane, mutum ne shi mai matukar kyau.

Ƙabilar Latuka: a wannan kabila, dole ne namiji ya sace duk matar da yake son aure daga baya sai ya sanar da mahaifinta

Yayin da a wasu sassan duniya, dole ne namiji ya fara neman yardar matar da yake son ya aura sannan ya ci gaba da neman amincewar iyayenta, al’ada ta sha bamban a garin Latuka na ƙasar Sudan ta Kudu.

A wannan ƙabilar, dole ne namiji ya sace duk wata ƙyaƙƙyawar mace da yake so sai ya sanar da mahaifinta daga baya
bisa al’adarsu, dole ne mai neman aure ya sace matar da zai aura, ta hanyar daukar wasu mazaje tare da wanda zai yi kwanton bauna, korarsu da kama matar.

Ana kai matar da aka kama zuwa gidan mai neman ta inda ake ajiye ta ba tare da son ran ta ba kafin mutumin ya sanar da mahaifinta daga baya.

Kamar dai duk waɗannan ba su da sha’awa sosai, dole ne mahaifin matar ya yi wa surukinsa duka don ya nuna cewa ya amince da auren da ya yi da ‘yarsa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]

Rubuta Sharhi