Ramar da na yi tana da alaka da ciwon mahaifiya ta, jinyar ta da kuma mutuwar ta, Jaruma Maryam Booth

  • Post author:
  • Reading time:6 mins read
You are currently viewing Ramar da na yi tana da alaka da ciwon mahaifiya ta, jinyar ta da kuma mutuwar ta, Jaruma Maryam Booth
Ramar da na yi tana da alaka da ciwon mahaifiya ta, jinyar ta da kuma mutuwar ta, Jaruma Maryam Booth

Fitacciyar jarumar Kannywood, Maryam Booth ta bayyana dalilin da yasa mutane suka ga ta rame har ake yi mata tambayoyi musamman masoyanta, inda tace yana da alaka da mahaifiyar ta.

A wata tattaunawa da BBC Hausa ta yi da ita a shirin Daga Bakin Mai ita, inda aka dinga jefa mata tambayoyi da dama dangane da rayuwar ta.

Ramar da na yi tana da alaka da ciwon mahaifiya ta, jinyar ta da kuma mutuwar ta, Jaruma Maryam Booth
Ramar da na yi tana da alaka da ciwon mahaifiya ta, jinyar ta da kuma mutuwar ta, Jaruma Maryam Booth

Ta fara da bayyana tarihin rayuwar ta inda tace asalin sunan ta Maryam Adamu, amma an fi sanin ta da Maryam Booth ko kuma Dijangala.

Ta ce an haife ta a ranar 28 ga watan Oktoban 1993, ta bayyana yadda ta yi makarantar Firamare a Ebony Nursery and Primary school da sauran makarantu. Ta yi karatun Diploma a jami’ar Bayero da ke Kano, sannan tawuce kasar Malaysia inda ta kara wata Diploma, ta yi digiri kuma yanzu haka ta a digirin digir dinta a can amma bata kammala ba.

Ta bayyana dalilin da ake hada mata sunanta da Booth, inda tace yana da alaka da mahaifiyar ta, ana kiran ta da Maryam Booth, ‘yar gidan Zainab Booth.

Ta ce ana yawan tambayar ta yaushe zata yi aure da kuma dalilin da yasa ta rame.

Ta ce aure lokaci ne, duk yadda mutum ya kai ga shirya wa idan lokaci bai yi ba babu yadda zai yi. Idan kuma lokaci ya yi sai abu ya tabbata.

Batun ramarta kuma, kada baki ta yi tace:

“Idan ka duba ramar da nayi, na dan gabannin lokaci ne, duk wanda ya sanni ya san alaka ta da mahaifiya ta kuma ya san zamantakewar mu.

“Rashin lafiyar ta da jinyar ta da damuwa da kuma rasa ta da nayi, dole na rame. Amma Alhamdulillahi dole na yi tawakkali.”

Ban so na sanya baki ba, amma naga cewa zargin da Naziru yake ba karamin abu bane – Maryam Booth

Jaruma Maryam Booth ita ma ta ce ba za a bar ta a baya ba, domin kuwa ita ma ta fito ta tofa albarkacin bakinta, inda ta bukaci Nazir ya kawo shaida idan har zargin da yake yi gaskiya ne…

A yayin da masana’antar Kannywood take ci gaba da ci da wuta, jarumai bila adadin sun fito sun tofa albarkacin bakinsu kan wannan lamari na zargi da ake yi musu na lalata da mata kafin su sanya su a fim.

Manyan jarumai irinsu Nafisat Abdullahi, TY Shaba, da dai sauran su sun fito sun nuna rashin jin dadinsu akan wannan zargi, duk da dai cewa ba wai sun karyata faruwar abin bane, amma sun koka akan yadda aka yi Nazir ya yi musu kudin goro.

Maryam Booth ta fito ta tofa albarkacin bakinta ita ma

Haka ita ma fitacciyar jaruma Maryam Booth ta fito ta tofa albarkacin bakinta kan wannan lamari, inda take cewa ba ta so ta fito tayi magana ba amma ganin cewa magana ce ake ta zina, hakan ya sanya ta ga dole ta fito tayi magana.

Maryam Booth ta ce wannan maganganu da Nazir yayi babban zargi ne da ba a daukar su da sanyi, musamman ma zargin zina da yayi.

Ta ce ita ba wai komai ne ya sanya ta magana ba, kawai dai ta ga cewa ita mace ce, kuma duk abinda ake magana a kai ya shafe ta, saboda haka dole ta fito ta tofa albarkacin bakinta.

Ta ce tana daya daga cikin mutanen da za su so su san wadanda suke irin wannan abu da yayi zargi a kai idan har ya tabbata abinda ya fada gaskiya ne kuma yana da hujja a kai.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Rubuta Sharhi