35.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Ku dauki makamai domin kare kanku daga ‘yan bindiga, jami’an tsaro sun gaza -gwamna ga ‘yan jihar sa

LabaraiKu dauki makamai domin kare kanku daga 'yan bindiga, jami'an tsaro sun gaza -gwamna ga 'yan jihar sa

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya buƙaci mazaunan jihar sa musamman waɗanda ke zama a ƙauyuka da su ɗauki halastattun makamai domin kare kawu nan su daga ‘yan ta’adda.

Ya bayyana cewa hakan ya zama wajibi ne  saboda yanzu an wuce da yayin cigaba da kiran neman ɗauki. Jaridar Daily Trust ta rahoto

Dole ne mu kasance cikin shirin ko ta kwana wajen tunkarar ‘yan ta’adda. Wannan wata hanya ce da zamu iya taimakawa jami’an tsaro wajen daƙile wannan matsalar tunda abubuwa sun yi musu yawa.

A cewar sa

Gwamnan ya magantu

Gwamnan, a wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai magana da yawun sa, Nathaniel Ikyur, yayi magana bayan an kai sabon hari da ya halaka mutum 5 a ƙauyen sa na Ndzorov a ƙaramar hukumar Guma da safiyar ranar Talata

Ya lissafo sunayen waɗanda lamarin ya ritsa da su kamar haka, Clement Tortiv, Enoch Utim, Terkimbi Kutaer, Mtaaega Tyogbea da kuma Aondoaver Swende.

Ya bayyana cewa wasu mutum biyu: Sunday Gaga da Torkwase Igbira sun samu raunuka a harin wanda ake zargin fulani makiyaya da ƙitsawa.

‘Yan sanda sun yi magana dangane da harin

Sai dai, kakakin hukumar ‘yan sandan jihar, SP Catherine Anene, yayin tabbatar da aukuwar lamarin, ta ce mutum huɗu aka halaka.

An tabbatar da aukuwar kashe-kashen da aka yi a Gbajimba, ƙaramar hukumar Guma. Mutum 4 sun rasa rayukan su yayin da mutum 1 ya ke amsar magani. Ana cigaba da gudanar da bincike.

A cewar Anene

A halin da ake ciki, shugaban ƙungiyar Miyetti Allah na jihar, Alhaji Risku Mohammed, ya bayyana cewa an sanar da shi dangane da lamarin yayin wani taro kan tsaro da gwamnatin jihar.

Ya bayyana cewa ya tuntuɓi mambobin sa sannan yana jiran yaji daga gare su ko suna da masaniya dangane da lamarin.

Yan bindiga sun yi awon gaba da amarya akan hanyar kai ta gidan miji a jihar Neja

Wata sabuwar amarya ta faɗa a hannun ‘yan bindiga akan hanyar kai ta zuwa gidan mijin ta a jihar Neja.

Jaridar Daily Trust ta samo cewa ‘yan bindigan sun kawo harin ne lokacin da ‘yan’uwan amaryar su ka ɗauko ta daga ƙauyen Allawa a ƙaramar hukumar Shiroro zuwa garin Pandogari, a ƙaramar hukumar Rafi ta jihar.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe