22.5 C
Abuja
Friday, December 2, 2022

Da ɗumi-ɗumi: Majalisa ta yi watsi da wani muhimmin ƙudirin shugaba Buhari

LabaraiDa ɗumi-ɗumi: Majalisa ta yi watsi da wani muhimmin ƙudirin shugaba Buhari

Majalisar dattawa tayi watsi da ƙudirin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari na neman yin gyara ga dokalr zaɓe ta 2022.

Ƙuɗirin dokar mai taken “Ƙudirin dokar da zai gyara dokar zabe ta 2022 da abubuwa masu alaƙa, 2022” wanda sanatoci su kayi watsi da shi, hakan ya sanya ƙudirin bai samu karatu na biyu ba. Jaridar Vanguard ta rahoto

An yi watsi da ƙudirin dokar ne yayin zaman majalisar na ranar Laraba.

Majalisa
Da ɗumi-ɗumi: Majalisa ta yi watsi da wani muhimmin ƙudirin shugaba Buhari. Hoto daga Vanguard

Kotu ta haramta yin gyara ga dokar zaɓen

Idan za a iya tunawa dai ƙudirin ya tsallake karatun farko ranar Talata duk da cewa akwai umurnin kotu wanda ya hana majalisar yin aiki akan sa.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya ƙalubalanci hukuncin kotun inda yake cewa ɓangaren shari’a bai da hurumin hana majalisar gudanar da ayyukanta wanda kundin tsarin mulki ya tanadar mata.

Kafin majalisar dattawan ta fara nazarin kudirin a ranar Laraba, Sanata Adamu Aliero, yayin da yake karanto doka ta 52 (5) na majalisar dattawa, ya bukaci Shugaban Majalisar da ya yi watsi da shawarar yin duba ga kudirin.

Shugaban majalisa ya dage sai an duba ƙudirin

Sai dai shugaban majalisar Ahmed Lawan ya dage kan cewa matsayar sa na cewa sanatoci ne kawai za su iya watsi da ƙudirin ba ɓangaren Shari’a ba wanda yake ƙoƙarin hana majalisar gudanar da ayyukanta.

Sai dai sanatocin sun kaɗa kuri’a inda su ka zaɓi hana sake karanta ƙudirin a karo na biyu.

Labari da ɗuminsa: Buhari ya rattaba hannu a kan gyaran dokar zabe

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya amince da ƙudurin dokar zaɓe na 2021 da aka daɗe ana jira.

Buhari ya ce ya kamata sabuwar dokar ta rage saɓani da rashin jituwa a harkar zaɓe, inda ya ce ya samu bayanai daga ɓangarori daban-daban domin tabbatar da cewa dokar ta yi yawa.

Shugaban ƙasar a shekarar da ta gabata ya ƙi amincewa da wani sabon salo na ƙudurin dokar saboda wasu dalilai da ya bayyana a cikin sakon sa ga majalisar dokokin ƙasar.

Sai dai ya sanya hannu kan ƙudurin dokar bayan da babban mai ba shi shawara na musamman kan harkokin majalisar dattawa, Sanata Babajide Omoworare, ya gabatar masa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labaunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe