24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Yanzu haka na shafa wa maza 119 da mata 19 cutar kanjamau, inji budurwar da ta kamu da cutar a 2016

LabaraiYanzu haka na shafa wa maza 119 da mata 19 cutar kanjamau, inji budurwar da ta kamu da cutar a 2016

Wata budurwa ‘yar Najeriya ta bayyana yawan mutanen da ta shafawa cutar kanjamau, bayan an tabbatar da tana dauke da cutar a shekarar 2016, LIB ta ruwaito.

‘Yar Najeriyar mai amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Twitter ta bayyana yadda a yanzu haka ta shafa wa kimanin maza 115 da mata 19, sannan tana cigaba da kirga.

Yanzu haka na shafa wa maza 119 da mata 19 cutar kanjamau, inji budurwar da ta kamu da cutar a 2016
Yanzu haka na shafa wa maza 119 da mata 19 cutar kanjamau, inji budurwar da ta kamu da cutar a 2016

Kamar yadda ta wallafa:

“Aminin dan uwana ne ya shafa min cutar a shekarar 2016 a lokacin ina ‘yar shakara 18 kacal.

“Shi ne mutumin farko da na yi lalata da shi har sai da na kai shekara 20. Tun a watan Disamba, 2017 da aka min gwajin cutar gami da tabbatar da cewa na kamu da ita, na lashi takobin shafa wa sauran mutane cutar da aka shafa min, ba tare da amfani kwararon roba ba.

“Kimanin maza 115 da mata 19 ne na shafa wa cutar, sannan ina cigaba da kirga. Tun daga lokacin, ban damu da mutuwa ba ko da yau ne. Menene amfanin rayuwa ta? Duk da na gama jami’a, bazan iya samun aiki ba saboda ina dauke da cutar kanjamau? Menene amfanin rayuwa ta idan sai na dogara da maza zan samu kudi? Menene amfanin rayuwa ta, idan sai na sha maganin ARV akai-akai don in rayu?

“A tunanin ku kuna da damar kira na azzaluma? Da ace kun san Ifeanyi, azzalumin abokin dan uwana, da kun san asalin siffar zalunci. Tunda babu wani banki a Najeriya dake son bani aiki, don kawai ina da cutar kanjamau, aikuwa dole in cigaba da yada cutar ga wasu.”

Ta ci gaba da cewa idan namiji ko mace ko ma ‘yar madigo baza ta iya danne sha’awar ta ba, ba za ta damu ba idan ta shafa mata sama da sau dari.

A cewarta:

“Hakan abu ne mai sauki a wuri na, ga jindadi da kuma taya ni dandanar bakin cikin da nake ciki.

“Ya dakile alakar mu bayan yi min alkawarin duniya da lahira. Tsabar damuwar da na shiga yasa na fadi wasu daga cikin darussa na a shekarar ta karshe a jami’a.

“Hakan yasa nayi manejin gamawa da digiri mai daraja ta biyu daga baya, ni da ya kamata in kammala da digiri mai daraja ta daya. Yanzu na ma gama amma na gaza samun aiki.”

Budurwa ta kwashe saurayinta da mari har sau 2 saboda ya nuna yana son aurenta a bainar jama’a

Wani saurayi da yayi yunkurin bawa budurwar shi mamaki wajen neman aurenta, amsar da ta dawo mishi da ita ba ta yi masa dadi ba, yayin da budurwar ba wai taki amincewa ba ne kawai, ta mayar da martani da duka ne.

Wani mai amfani da shafin sadarwa na Twitter, mai suna @EazyKel_who yaa wallafa bidiyon yadda wannan lamari ya faru a shafinsa, inda ya caccaki mutumin kan dalilin da ya sanya ya nemi auren budurwar tashi a bainar jama’a.

Neman auren bai yiwa saurayin yadda yake so ba

Yayin da aka nuno saurayin ya durkusa a gaban budurwar, ga kuma cake a kan tebur inda budurwar take zaune, an gano budurwar ta tashi tsaye ta kwashe shi da mari, inda take tambayar shi dalilin da ya sanya shi ya zo wajen.

Duk da kokarin da mutane suka din yi wajen ganin sun shawo kan budurwar, budurwar ta kara kwashe saurayin da mari a karo na biyu a yayin da yake tsugunne a gabanta.

Daga baya kuma ta dauki wannan cake da ya kawo ta jefe shi da shi, hakan ya sanya kayan jikin shi suka lalace, duka dai saurayin yana tsugunne a gaban ta bai tashi ba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe