35.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Abubakar Mai Shadda da Jaruma Hassana sun saki zafafan hotunan kafin auren su

LabaraiKannywoodAbubakar Mai Shadda da Jaruma Hassana sun saki zafafan hotunan kafin auren su

Tun bayan bayyanar labarin auren masoyan guda biyu, fitaccen furodusa Abubakar Bashir Mai Shadda da Jaruma Hassana Muhammad mutane suka kosa su ga hotunan auren su.

Tuni shirye-shirye suka fara nisa don har lefen auren su ya bayyana wanda kowa ya shaida cewa ya kashe makudan kudade.

prewadding pic1
Abubakar Mai Shadda da Jaruma Hassana sun saki zafafan hotunan kafin auren su

Tun ranar Litinin wani bidiyo ya dinga yawo na kafin auren su wanda mutane suka dinga cece-kuce akan shi.

A ranar Laraba da safe kyakkyawar jarumar ta saki hotunan kusan guda goma a shafin ta na Instagram wadanda suka ja hankalin mutane da dama.

Auren su ya yi matukar daukar hankali saboda dama ana ta rade-radin cewa ‘yan fim ba sa auren juna.

Da alamu wannan auren zai karyata surutan jama’a don su biyun sun nuna wa duniya tsananin so da shakuwar su.

Tuni abokar sana’ar su suka fara wallafa hotunan tare da yi musu fatan alkhairi.

Muna musu fatan samun zuri’a dayyiba.

Bayyanar bidiyon kafin auren Furodusa Mai Shadda da amaryar sa yana rungumar ta ya tayar da kura

Fitaccen furodusan Kannywood, Abubakar Bashir mai shadda yana shirin angwancewa da jaruma Hassana Muhammad kamar yadda shi da ita suka sanar a shafukan su ta hanyar wallafa hotunan katin gayyata.

Baya ga wannan, ya wallafa bidiyo na jerin akwatuna 17 na auren su wanda yayi mata a matsayin lefe, hakan ya sa mutane suka tabbatar da cewa shirye-shiryen aure ya yi nisa.

Sai dai a ranar Litinin da yamma wani bidiyo ya karade shafukan sada zumunta wanda aka ga yana rungumar ta da alamun hotunan kafin aure zasu yi, wato Pre-wedding pictures.

Hakan ya yi matukar janyo cece-kuce inda mutane suka dinga suka tare da alawadai akan bayyana alfashar da suka yi.

Kasancewar aure bautar Ubangiji ne, wasu suna ganin bai dace a saba masa ba yayin shagulgulan musamman idan aka yi la’akari da cewa su biyun sanannu ne kuma suna ikirarin fadakarwa suke yi a fina-finai.

Shafin Dokin Karfe Na Facebook ya wallafa bidiyon wanda fiye da mutane dubu 31 suka gani. Sannan daruruwan mutane sun dinga tsokaci daban-daban.

LabarunHausa.com ta tattaro wasu daga cikin tsokacin jama’a:

Wani Abdullahi Yakasai yace:

“Ma su koya Tarbiyya a kasar Hausa kenan…”

Wata Maman Nana ta kada baki ta ce:

“Dagani sun Saba yin haka da juna
Tunda Babu alamar kunya atare da suAllah ya shiryemu baki daya.”

Habiba Yusuf Aliyu ta yi tsokaci inda tace:

“Allah kada kabamu ikon saɓama ka don mu burge duniya, Allah kaqara shirya zuri’ar musulmi.”

Albishir Gobe Qiyamar Fadakarwa yace:

“Haramunne kakama mace ko ita takamaka ba tare ka mallaketaba ina nufin batareda ka auretana lallai wannan mummur dabi’ar zuciya ce Allah yakiyashemu Amiiiiiiiiiiiiin
Allah yashiryamu daku amin
Tabbas wannan barnan dakuka kullomana da ita inde bakutsayananba wallahi zamuyi mummunar Addu”o”i akanku Allah yasa mugane mukuma gyara Amiiiiiiiiiiiiin.”

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe