Zaɓen 2023: Dole ne shugaban ƙasa ya fito daga kudancin Najeriya -wata ƙungiya ta magantu

  • Post author:
  • Reading time:5 mins read
You are currently viewing Zaɓen 2023: Dole ne shugaban ƙasa ya fito daga kudancin Najeriya -wata ƙungiya ta magantu

Wata ƙungiya mai suna Defense for Yoruba People’s Rights, tayi kira da jam’iyyun Peoples Democratic Party (PDP) All Progressives Congress (APC) da sauran jam’iyyu kan cewa su zaɓo ɗan takarar shugaban ƙasa a zaben 2023 daga yankin kudancin Najeriya.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Otunba Muyideen Olamoyegun, ya fitar a birnin Akure, na jihar Ondo ranar Talata. Jaridar Punch ta rahoto

Adalci ne kai kujerar yankin kudu

Ƙungiyar ta bayyana cewa yin adalci ne kai kujerar shugaban ƙasa yankin kudu, inda ta jajirce cewa lallai dole ne jam’iyyun APC, PDP da sauran jam’iyyu su zaɓo yan takarar su daga yankin kudu domin tabbatar da daidaito.

Ƙungiyar kuma tayi gargaɗi akan yan takarar shugaban ƙasa da su ka fito daga yankin kan cewa kada su kuskura su amshi matsayin mataimakin shugaban ƙasa daga kowace jam’iyya, yin hakan a cewar su zai fusata mutanen yankin.

Sanarwar na cewa:

“Mun faɗa cewa mutanen yankin kudamcin Najeriya za su ɗauki duk wani ɗan takarar shugaban ƙasar da ya amshi matsayin mataimakin shugaban ƙasa daga kowane ɗan takara a matsayin butulu. Abinda kawai mu ke so shine shugaban ƙasa.

Yankin kudancin Najeriya yana da ƙwararrun ‘yan siyasan da za su iya ƙarbar ragama daga hannun shugaba Muhammadu Buhari, sannan su tafiyar da jagorancin ƙasar nan cikin nasara.

Ƙungiyar tayi babban roƙo

Ƙungiyar kuma ta roƙi ‘yan siyasa da su zaɓi ɗan takarar da su ke so wanda ya fito daga kudancin Najeriya, inda ta buƙaci masu yin zaɓe da su yi zaɓe cikin hikima.

Mu na rokon jama’a da su tabbatar sun yi amfani da hankalin su wajen zaben shugaban ƙasa domin tabbatar da goben ƴaƴan mu tayi kyau.

Akwai matukar wahala wajen ceto yankin kudancin Najeriya daga wariyar da ake nuna wa yankin saboda yankin ya kasa magana da murya ɗaya akan ƙaƙaba ‘yan takara da ake yi a zaɓukan baya.

Zaben 2023: Cancanta za mu bi wajen zaɓar shugaban ƙasa -inji dattawan arewa

Ƙungiyar dattawan arewa ta tabbatar da cewa yankin arewa zai zaɓi ɗan takarar shugaban ƙasa wanda ya cancanta ne, ba tare da yin la’akari da yankin da ya fito ba, a babban zaben 2023 mai zuwa.

Ƙungiyar ta ci alwashin ba zata sake maimaita kuskuren zaɓar kowane irin ɗan takara ba, kamar yadda aka yi wurin zaben shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2015 bisa bin son zuciya, jaridar independent.ng ta ruwaito.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]

Rubuta Sharhi