KUYI RAJISTA : Hukumar Soji ta Najeriya ta fara daukar ma’aikata

You are currently viewing KUYI RAJISTA : Hukumar Soji ta Najeriya ta fara daukar ma’aikata
Hukumar Soji ta Najeriya ta fara daukar ma'aikata

An bude shafin yanar gizo na hukumar soji ta Najeriya ga masu son suyi rajista.


Damar zata mai da hankali wajen daukar cikakkun sababbin ma’aikata har guda 83 daga cikin maza da mata.


Haka kuma, damar ta fara ne daga 7 ga watan Maris, zuwa 13 ga watan Mayu na shekarar 2022. Ana bukatar masu sha’awar shi, su tanadi wadannan ka’idodi da za’a ayyano : 

(1) Dole ne mai neman shiga ya kasance bashi da aure, kuma ya kasance haifaffen Nageriya mai dauke da katin shaidar zama dan kasa/ lambar NIN ko lambar BVN. 

(2) Wajibi ne ya zama mai koshin lafiya a jikin sa, da  kwakwalwar sa, kamar yadda yake a tanadin ka’idodin aikin sojin Nageriya. 

(3) Tilas ya zama bai taba gurfana a gaban kotu domin tuhumar sa da aikata wani laifiba. 


(4) Dole ne ya kasance ya mallaki sahihiyar takaddar shaida ta haihuwa, wadda hukumar gididdigar kidaya ta kasa ta tabbatar da sahihancin ta ko asibiti, ko karamar hukuma, ko kuma sahihiyar takaddar shaidar kotu. 

najeriya
Hukumar Soji ta Najeriya ta fara daukar ma’aikata

(5) Wajibi ne ya zamto masu neman shiga, su mallaki takaddar shaidar kammala sakandare kamar WASCE/GCE/NECO/ da kuma NABTEB, wanda ke dauke da akalla Pass guda hudu wadanda aka samesu a zama da bai wuce guda biyu ba. 


(6) Dole ne kada shekarun mai nema su gaza 18 sannan kuma kada su wuce 22 izuwa ranar da za’a fara bada horo wadda ta kama 8 ga watan agusta. 


(7) Dole kada tsayin mutum ya gaza mita 1.68 da kuma mita 1.62, ko mace ko namiji baki daya. 
(8) Dole ne mai nema ya mallaki sahihiyar takaddar zama cikakken da jihar da ya fito. 

(9) Karin ilimi a wasu fannin, zai kara wa mai nema daraja ta musamman. 


(10) ga duka masu bukatar cikewa sai su dannan wannan adireshi.

Sojojin Najeriya sun fatattaki ‘yan ta’addan ISWAP, sun kwato awaki 500

Dakarun sojojin Najeriya na Operation Hadin Kai a jihar Borno sun yi nasarar ƙwato awaki 500 a hannun ‘yan ta’addan ƙungiyar Islamic State West Africa Province (ISWAP) a ƙaramar hukumar Jere ta jihar Borno.

Jaridar Daily Trust ta samu cewa anyi ‘yar gajeruwar musayar wuta tsakanin sojin da ‘yan ta’addan na ISWAP, wacce ta yi sanadiyyar mutuwar wasu daga cikin mambobin ‘yan ta’addan.

Wata majiya ta bayyana cewa makiyayan sun turo saƙon neman agajin gaggawa ga kwamandan rundunar atisayen Lafiya Dole, Major General Chris Musa, inda su ka sanar da shi satar awakin da aka tafka musu.

Sojojin sun bi bayan ɓarayin awakin inda su ka ritsa su a kusa da wata gonar cashew. Sun yi musayar wuta da su wacce ta yi sanadiyyar mutuwar biyar daga cikin su, yayin da sauran su ka ranta ana kare su ka bar awakin. Majiyar sojin ta tabbatar

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]

This Post Has 4 Comments

 1. Hassan A Suleiman

  Ina gaida ma aikatan Nigeria gaba daya

 2. Shamsu usman

  Tasro

 3. Aliyu yakubu

  Slm ina menuna farincikina dakasantuwar haka kuma ina godiya wa Allah dayaba wa dakarun sojin kasata masu kishin kasa iko da damar aiwatar da akin su cikin kwarewa ina fata Allah yabasu sa ah damu masu niyyar shugowa yanzu I want to be a Nigerian army I proud of the Nigerian army

 4. Usman sulaiman

  Thanks

Rubuta Sharhi