Furodusa Champagnebeatz yace ba shine mahaifin ‘yayan sa guda 3 da matarsa ta haifa masa ba

You are currently viewing Furodusa Champagnebeatz yace ba shine mahaifin ‘yayan sa guda 3 da matarsa ta haifa masa ba
Furodusa Champagnebeatz yace ba shine mahaifin 'yayan sa guda 3 da matarsa ta haifa masa ba

Shararren mai daukar nauyin kade-kade da wake-wake Champagnebeatz, ya ja hankalin yan Nageriya da dama a yanar gizo, inda ya zargi matatar sa da mahainciy

Furodusan, a wani bidiyo da Insatastoty suka saki, ya bayyana cewa, ya gano ba shine uba mahaifi na jini ga ‘yayan sa har guda uku da matar tasa ta haifa masa ba. 


Labarin furodusa Champagnebeatz din shine wanda a halin yanzu yake yamutsa hazo a yanar gizo, inda yan kasa kowa yake fadar albarkacin bakin sa. 


Wani Furodusan kade-kade da wake-wake dan Nageriya, mai suna   Champagnebeatz ya sha martani a dandalin yanar gizo, bayan wani al’amari mai girma da ya wallafa a shafinsa na instagram, a ka iyalin sa. 


Furodusan a wani sako da ya saki a shafin Insatastory, yace a wani bincike da ya gudanar ya gano cewa ba shine mahaifin ‘yayan sa guda uku ba, wadanda suka samu shi da matarsa. 

Champagnebeatz
Furodusa Champagnebeatz yace ba shine mahaifin ‘yayan sa guda 3 da matarsa ta haifa masa ba

Champagnebeatz din ya lissafo sunayen  ‘yayan kamar haka : Favour, Donald da kuma Richard, inda yake zargin matarsa da yin lalata da wasu mazan a waje. 


Abin da ya rubuta :

“Abu ne mai matukar girgiza zuciya da na gano cewa   Yemi Adebowale, tana alaka da wadansu gayu a waje, tare da cewa muna da alakar aure da ita, inda ni kuma take yaudara ta da cewa nine uban yayan ta har guda uku” 

Ya fada


Mutane sunyi ta sharhi kalakala akan lamarin 

thisiskingx yace :

“Gwajin kwayoyin halitta na DNA ya zama wajibi ne…..bazamu bar wannan ya wuce be dan uwa… #justiceforbro ” 

thathoneygirl_kitchen yace :

” ‘Yaya uku? Haba kai, lallai wannan abin kaduwa ne ” 


nnenna_aldo Yace :

” Dan Allah idan baku da wadataccen imani kada kuyi aure, idan kuma kunga mutum baiyi aure ba to kada ku dinga ingiza shi yayi har sai yaji da kansa yana da sha’awar yi. Wannan abin bakin cikine.”

beyond_intimacy yace :

“Maimakon yin haka me zai hana kawai ka zama uwa da uban gaba daya”

 

ronkeyzee yace : 

” Gaskiya wannan abin kaduwa ne, babu wani mutum da ya cancaci a yi masa haka. Wasu matan ehhhhh ahhhhh, nama rasa abin da zance “

Maha’inciyar Uwa : mai jama’a Pretty Mike ya shawarci mazaje 


Tun farko, Legit.ng, sun  ruwaito cewa, wani dan Nageriya Pretty Mike ya shawarci mazaje da su dinga dubawa ya tabbatarda cewa ‘yayan sa basa kama da wani daga abokan aikin matar sa.

Saurayi ya yaudari budurwarsa bayan ta bashi kodar ta guda 1 an dasa ya samu sauki

Colleen Le budurwa ‘yar shekara 30, wadda take zaune a kasar Amurka, ta bayyana cewa saurayinta a wani lokaci a baya ya bukaci ayi masa dashen koda, saboda yana fama da ciwon koda mai tsanani, wanda ya sanya ake yi masa wankin kodar yana dan shekara 17.

Ta amince ta sadaukar masa da warin kodarta bayan likitoci sun tabbatar da cewa zata yi daidai da ta shi. Bayan an gama aikin ya samu lafiya, ‘yan watanni kadan sai ya ci amanarta ya gudu ya barta.

Colleen wacce take tauraruwar tiktok, ta sami dumbin masu sharhi a kan bidiyon ta da ta wallafa, wanda ta nuna jerin abubuwan rashin kyautawa da yayi mata, inda da yawa suka dinga yaba mata saboda ceto ransa da tayi kuma suna nuna ma bata dace da shi ba.

A bidiyon ta na farko, Colleen ta bayyana cewa tsohon saurayinta ya gaya mata cewa kodarsa tana aiki ne kasa da kashi biyar cikin dari.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]

Rubuta Sharhi