Kwararan darussan da labarin Annabi Sulaiman ya koya mana

You are currently viewing Kwararan darussan da labarin Annabi Sulaiman ya koya mana
Kwararan darussan da labarin Annabi Sulaiman ya koya mana

Lallai Kurani mai girma ya kawo cikakken tarihin Annabi Sulaiman da sarauniya Bilkisu, wanda tabbas ya gayamana mahimmancin sa da kuma abin da labarin yake koyawa. Saboda haka me zamu iya cewa mun koya daga labarin Annabi Sulaiman din da sarauniya Bilkisu? 


Toh ! Farko da idan mun kula da yadda martanin sarauniya Bilkisu ya kasance, a yayin da aka sanar da ita dangane da sakon musulunci ; ita da farko abin da tayi tsammani wata yaudara ce.

Nuna shakkun sarauniya Bilkisu ga gayyatar Annabi Sulaimanu

A lokacin da dan aiken Annabi Sulaiman ya je mata, sai ta dinga shakka aka niyyarsa a gareta. Tabbas ta dinga tunani cewa anya kuwa wani zai iya yi mini wa’azi akan Ubangiji kuma yace yana yin hakan ne domin amfanin kai na. 


Kai  ! Dole akwai wata boyayyar manufa. Ba irin haka muke ji ba idan ana yi mana wa’azi? ” To dan me suke gayyata ta zuwa musulunci? Me suke Bukata ?. 


A Wannan duniyar wani ya kashe makudan dukiya kawai dan wani ya ji dadi? Ha ! Gaskiya wannan bakon abune ace wasu mutane wai su gayyace mu domin mu san wani abu akan addinin musulunci, kuma duk ba dan wani dalili ba sai domin su isar da  sako, Toh !. 


Amma fa mu sani, shi fa Annabi Sulaiman har cikin zuciyar sa babu wata manufa da ya boye bayan isar mata da sakon Allah. Kawai yana so ne ya tsamo Bilkisu daga duhun kafirci. 

sulaiman
Kwararan darussan da labarin Annabi Sulaiman ya koya mana


Kuma dama abin da yafi kyau gareta kenan. Wato ta kauracewa bautar rana, wata, da kuma taurari. Maimakon haka ta koma bautar wanda ya halicci sammai da kasa da abin dake tsakanin su shine Allah SWT. 


Wani darasin kuma da yake cikin labarin, shine yadda Annabi Sulaiman ya kalli kyaututtukan da aka kawo masa. Ha ! Me zai yi da wasu zinare da gwala-gwalai? Cewa yayi,

abin da aka bamu na imani da Allah yafi alkhairi daga abin da aka baku na dukiya “. 


Darasi na karshe, shine meka wuya ga muradin Allah da sarauniya Bilkisu ta yi. Bayan duk wadannan abubuwan da suka faru, a karshe sai sarauniya Bilkisu tace ta sallama ta meka wuya ga addinin Allah. 

Mika wuyan sarauniya Bilkisu


Wannan kyakkyawar shawara data yanke, ta janyo mata samun nutsuwa a zuciyar ta da rayuwar ta. Hakan abune mai matukar sauki amma ga wadansu, ya zamo mai wahalar gaske. 


Labarin Annabi Sulaiman, ya koya mana cewa, meka wuya ga Allah yafi alkhairi akan mallakar tarin gwala-gwalai da zinare, ko kuma maduduwar dukiya.

Tarihin Annabi Sulaiman da Sarauniyar Bilkisu Mai Gadon Zinare

Annabi Sulaiman, mutum ne wanda a rayuwar sa akwai bangarori guda uku wadanda suke koyar da dimbin darussa a rayuwar dan Adam. 

Bangaren farko na rayuwar sa, shine kasantuwar sa babban sarki mai mulkin mutane da aljanu, inda a wannan bangaren yake da ajizantakarsa irin ta dan Adam kamar kowanne irin mutum. 

Soyayyar sa da dawakai itace sanadin faduwar mulkinsa, tunda tayi sanadiyyar shagaltar dashi wajen mantawa da wata ibada. 

Baiwar Annabi Sulaiman

Haka kuma, Annabi Sulaiman yana iya jiyo wata siririyar murya, (ta tururuwa) wadda ta tunatar da shi wajen biyayya ga Allah. Sannan daga karshe an sake dawo masa da mulkinsa daya kufce masa. 

Wani bangaren na rayuwar Annabi Sulaiman shine baiwar da aka bashi ta iya magana da dabbobi da tsuntsaye, da kuma baiwar sarrafa iska, wanda akan wannan ne labarin mu zai mai da hankali akai. 

Annabi Sulaiman, yana da gagarumar rundunar mutane, aljanu, da kuma tsuntsaye.
 Dukkan musulmai sunyi imani cewa aljanu wasu halittune da Allah ya halitta, cikin su akawai masu kirki da marasa kirki, wadanda  ba’a iya ganin su a fili. 

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]

Rubuta Sharhi