Yawancin ‘yan fim warin baki gare su, Jaruma Angela Eguavoen ta fasa kwai

  • Post author:
  • Reading time:6 mins read
You are currently viewing Yawancin ‘yan fim warin baki gare su, Jaruma Angela Eguavoen ta fasa kwai
Yawancin 'yan fim warin baki gare su, Jaruma Angela Eguavoen ta fasa kwai

Fitacciyar jarumar fina-finan kudu, Angela Eguavoen ta ce abokan sana’arta maza suna fama da warin baki, Pressinformant.com ta ruwaito.

Yayin tattaunawar da akayi da ita a ranar Asabar, ta bayyana cewa yayin da ake umartar ta da sumbatar abokan aikin ta idan suna shirya fim, tana haduwa da masu warin baki. Amma ta ce akwai wasu masu tsafta.

Yawancin 'yan fim warin baki gare su, Jaruma Angela Eguavoen ta fasa kwai
Yawancin ‘yan fim warin baki gare su, Jaruma Angela Eguavoen ta fasa kwai

Kamar yadda ta kada baki ta ce:

“Akwai jarumai maza da dama da ban ji dadin sumbatar su ba. Idan ka hadu da mai warin baki gaskiya babu dadi. Na fuskanci irin hakan kwarai da gaske.

“Har ila yau akwai masu tsafta sosai da na yi aiki da su yayin shirya fina-finai. Gaskiya hakan ya kayatar da ni.”

Yayin da aka tambaye ta nata ra’ayin dangane da mata masu amfani da asiri wurin mallakar namiji, ta ce hakan yana faruwa a masana’antar.

Kamar yadda Angela tace:

“Amfani da asiri wurin mallakar namiji babban kuskure ne. Hakan yana nuna tsananin rashin sanin ciwon kai. Ba zan taba ba wata shawarar aikata hakan ba. Duk bala’i kada mace ta yi amfani da asiri wurin rike namiji. Idan ta kwantar da hankalin ta sai ta hadu da wanda ya fi shi.”

Har ila yau, jarumar tayi magana akan matan da ke zuwa asibiti don likitoci su kara musu mazaunai inda tace in har mace tana da wannan kudin ta je ta yi abinta.

In har hakan zai sa mace farin ciki, zata iya zuwa ta yi inji jarumar. Amma dai ita bata yi ba kuma bata da shirin yin hakan.

Amma kila idan ta haihu taga bukatar hakan ta lallaba ta je ta yi abin ta.

An harbe jarumar fim har lahira yayin da tauraruwar ta ke kan haskawa

Yan bindiga sun harbe wata jarumar fim ta kamfanin fina-finai na Nollywood wadda aka fi sani da Ngozi Chiemeke, a ranar 8 ga watan Disambar shekarar 2021.

A cikin rahotannin da aka samu kan lamarin, sunce kisan ya faru ne a titin deeper life dake garin Boji-Boji Owa a karamar hukumar Ikar Arewa maso Yamma ta Jihar Delta.

An kashe jarumar fim din a wajen sana’arta ta POS

A rahoton da Mujallar Fim ta fitar, ta gano cewa an kashe jarumar wacce take kan ganiyar tashenta, a fina-finan Nollywood, a cikin shagon da take sana’arta ta shiga da fitar kudade, wato POS.

Yan unguwar da abin ya faru a kusa dasu, sunce, sunji karar rashin bindiga, amma koda suka rugo don su kawo dauki, basu tarar da kowa a wajen ba.

Babu wanda ya san abin da yasa aka yi kisan, domin har ya zuwa lokacin da aka dauketa daga wurin, babu wata shaida da zata nuna alamun wadanda keda hannu wajen wannan aika-aikar.

Mutane sun shiga rudani sakamakon kisan jarumar

Kisan jarumar, ya haifar da gagarumin rudani a cikin jama’ar garin, abin da yasa suka rika jinjina kisan gillar da aka yima jarumar, inda aka dauketa aka kaita dakin ajiye gawa domin cigaba da bincike.

A Jawabin jami’in yada labarai na hukumar ‘yan sandan jihar ta Delta, DSP Bright Edafe, ya bayyanawa manema labarai cewa tabbas labarin kisan jarumar ya iske rundunar tasu, inda ya tabbatar da cewa,

“Wasu maza da ba’a san ko su waye ba sune suka hallaka matashiyar jarumar. Amma sun fara fadada bincike domin kamo duk masu hannu akan kisan matashiyar jarumar dan gurfanar dasu a gaban shari’ah”.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Rubuta Sharhi