ISIS FYADE : Yadda ‘yan ta’addan ISIS suka yi min fyade har sau 180 – Inji wata yarinya ‘yar Yazidi

You are currently viewing ISIS FYADE : Yadda ‘yan ta’addan ISIS suka yi min fyade har sau 180 – Inji wata yarinya ‘yar Yazidi

Yazidi sunan wata kungiyar addini ce wadda suke zaune a Arewacin Iraq. Abin takaicin shi ne, an takura musu matuka ta yadda suke tserewa domin tsira da rayuwar su.

An karkashe maza da dama, matan aure da yan mata kuma sai ‘yan ta’adda suka kama su lokacin da suka farmaki Sinjar a watan Agustan shekarar 2014. 

Yadda yan ta’addan ISIS din suka tsara mutanen


Yan kungiyar ta’addan ISIS, sunyi kafar rago ga mutane  ‘yan Yazidi kimanin mutum dubu hamsin 50,000

Mutanen basu da matsera babu abinci babu ruwan sha da zasu rayu. Da yawa daga cikin su sun rasa ransu a kokarin  hawa kan dutsen Sinjar domin tsira. 

3634 Ekhlas A Yazidi girl explains how she was raped 180 times as sex slave by ISIS 02 removebg preview 1
Yariyar da ISIS Suka yiwa fyade har sau 180

Kamar yadda aka fada a baya, an karkashe maza da dama an kuma kama matan aure da yan mata. Wadannan matan an sanya su a kangin wahala iri-iri. Suna ganin muzanci karara, inda ake cin zarafin su ta fuakar lalata da su. 


Ekhlas daya ce daga cikin matan da aka kama, kuma ta bayyana labarin yadda yan ta’addan suka dinga yi mata fyade. 

Yadda yan ta’addan suka yi mata fyde har sau 180


Marainiyar yarinyar, ISIS sun kamata ne tun tana shekara 14. Da take magana da tashar BBC, ta bayyana cewa anyi mata fyade har tsawon wata shida, gamida da azabtarwa da muzantawa a bainar jama’a, wanda har sai da ta dinga tunanin kashe kanta. 


A cikin wadanda aka kebe akan dutsen Sinjar har da ita Ekhlas din, masu aikin ceto ne suka yi kokarin tseratar da su, amma ita Ekhlas bata iya tairaba, inda aka kara kamata. 


An sake dawo da ita gurin yan ta’addan, ba ita kadai bace a can gurin, akwai mata akalla 150, sai wanda ya kamata ya zabeta a cikin su dari da hamsin 150. 


Da take bayyana wanda ya kamata, tace mutumne mummuna wanda muninsa ya kai bata iya hada ido dashi. Yana da dogon gashi, kuma koda yaushe wani wari yake yi a jikin sa. 


Budurwar ta nuna alamar bacin rai da kaduwa yayin da take bayyana wanda ya ci zarafin ta ya dakile mata duk wani ‘yanci da walwala. 


A fadar ta, ta so ace ta make mai tsaron ta ta gudu daga  wurin, amma bata da kowanne irin makami, ita murmurin ta kawai shi ne kadai abin da ya rage mata. 

Miji ya bawa matar sa kwaya ya gayyato abokin aikin shi ya yi mata fyade akan idon shi

An yanke hukuncin zama gidan kaso na shekaru 3 ga wani mutum bayan yayi yunƙurin yin fyade ga matar abokin aikin sa, wacce mijinta ya gayyace shi domin yin wannan ɗanyen aiki.

An faɗi wannan labarin mara daɗin ji ne a kotun ƙolin kasar Singapore cikin wannan makon.

An sakaya sunayen su saboda tsabar munin laifukan da suka aikata.

A shekarar 2017, mutumin mai shekaru 47, ya amsa gayyatar da abokin aikin sa yayi masa ta zuwa gidan sa domin yin fyaɗe ga matar sa, Channel News Asia ta ruwaito.

Sun ba matar kwayoyi da giya, sannan mijin yana kallo yayin da mutumin ya ci zarafin matar tasa.

Abin ban tsoron shi ne yadda yaran matar guda uku da mai aikin gidan suke kwance suna barci a wani ɗaki daban lokacin da lamarin ya auku.

Sai dai, mutumin wanda yayi yunƙurin yin fyaɗen, jikin sa ya dakatar da shi inda ya samu matsalar rashin tashin mazakutar sa wanda hakan ya sanya dole ya kasa ƙarasa aikata laifin.

Ya amsa laifin tuhumar da ake masa ta bada haɗin kai wajen aikata fyaɗe, inda bai kai ga aikatawa ba, sai kuma laifin keta haddi.

Matar ta samu ramuwar gayya, inda ta buƙaci mijin ta da abokin aikin sa, su rubuta takardar iƙirarin aikata laifin, wacce kuma su ka rubuta.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@alamfas

Rubuta Sharhi