Ni musulmi ne mai tsoron Allah don haka Allah ya isa tsakani na da kai, Martanin Turji ga Sheikh Bello Yabo

  • Post author:
  • Reading time:6 mins read
You are currently viewing Ni musulmi ne mai tsoron Allah don haka Allah ya isa tsakani na da kai, Martanin Turji ga Sheikh Bello Yabo
Ni musulmi ne mai tsoron Allah don haka Allah ya isa tsakani na da kai, Martanin Turji ga Sheikh Bello Yabo

Fitaccen dan bindigar nan wanda ya addabi yankin Zamfara ya ce shi musulmi ne mai tsoron Allah, kuma yana yin sallolinsa biyar don gudun fushin Ubangiji.

A wata tattaunawa da Aminiya ta yi da shi, ya ce malam Bello Yabo ya yi masa kazafi kuma sai Allah ya saka masa.

turji1
Ni musulmi ne mai tsoron Allah don haka Allah ya isa tsakani na da kai, Martanin Turji ga Sheikh Bello Yabo

A cewarsa shi cikakken musulmi ne mai gudun fushin mahaliccin sa.

Kamar yadda ya bayyana a bidiyon, da farko ya fara da cewa:

“Ko wanne malami ne toh, ka san mutane da yawa suna cewa bamu bin addini. Cikin ayar Al’qur’ani akwai inda Allah yake cewa ‘innad dina indallahi islamu’, duk musulmi ya san wannan ayar.”

Ya ci gaba da cewa duk malami ya san da wannan ayar kuma wanda bai san ta ba ba zai iya kawo ta ba.

Ya ci gaba da cewa duk wanda yace ba sa bin addini toh addinin ba na shi bane. Na Allah ne don shi ne ya halicce kowa ne. Kuma idan sun yi addinin ba lallai malamin ya gane ba.

Ya ci gaba da cewa:

“Masallaci ka taras da ni kuma ba kai na yi wa sallah ba, Allah na yi wa. Saboda ina gudun haduwa ta da shi.”

Ya musanta batun Sheikh Bello Yabo wanda yace Turji ba musulmi bane, inda yace duk wani abu da Ubangiji ya umarta musulmi yayi, yana yi.

Bi’izinillahi duk dan takarar da Buhari ya daga hannun sa sai mun kayar da shi – Sheikh Bello Yabo

A daidai lokacin da aka fara buga gangar siyasa a Najeriya, ‘yan siyasa da dama sun fara fitowa suna baja kolin kansu ga al’ummar Najeriya, musamman ma wadanda suke da burin fitowa takarar shugaban kasa.

Zuwa yanzu dai an samu manyan ‘yan siyasa da dama da suka fito suka nuna ra’ayinsu na fitowa takarar shugaban kasa, wadanda suka hada da tsohon gwamnan jihar Lagos, kuma jigo a jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, tsohon gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha da dai sauran su.

Sheikh Bello Yabo ya caccaki ‘yan siyasa

A wannan karon shahararren Malamin nan ne na addinin Musulunci na jihar Sokoto, Sheikh Bello Yabo ya fito yana caccakar ‘yan siyasar, da kuma nuni ga al’umma akan irin shugaban da ya kamata al’umma su zaba.

A cikin maganganun na Malamin da muka ci karo da su a wani bidiyo da aka wallafa a shafin Facebook na Sheikh Al-Bani Sheikh Jaafar ya bayyana cewa, duk wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi tsautsayin tsayarwa takara sai sun kayar da shi, ga dai kadan daga cikin abinda Malamin ya ce:

“Yanzu an kusa kada gangar siyasa, gwamnatin da ta wuce ta PDP karkashin jagorancin Goodluck Jonathan, ta karye ne saboda sun kyale ana kashe mutane.

“To abinda ya ci waccan gwamnti haka ita ma wannan gwamnatin zai ci ta, saboda haka sun riga sun yi hasashen hakan.

“Bari na fadi wani sirri wanda da yawan mutane basu san da shi ba, a baya ana rudar mutane ana cewa lokacin da Buhari ya hau mulki wasu kananan hukumomi a jihar Borno suna hannun Boko Haram, Wallahi karya ne. Lokacin da Buhari ya hau mulki babu karamar hukuma daya dake hannun Boko Haram.

“Lokacin da zabe ya zo kusa a wancan lokaci, aka ga cewa babu wata mafita, sai aka yiwa Jonathan magana, aka ce masa akwai wasu garuruwa a hannun Boko Haram, saboda haka zabe ba zai yiwu ba a wannan yankin, koda ma a ce ya yiwu ba za a zabe mu ba, saboda haka ka tashi kayi wani abu.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: Legit.ng

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]

Rubuta Sharhi